ALJANAR FATIMA 7 To 12 Hausa Novels

 


👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 7-8



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽




THIS PAGE IN DEDICATED TO YOU.



_*QUEEN HAUWANCY AUTAR MARUBUTA*_ 🤓



_I love you to the moon and back, and you know that. I will never let you down, even if you make me mad, you can always ask me advice, I will never leave you._



💃🏻💃🏻 ```Duk illahirin yan writers na zamani suna ji dake yar auta kaman yanda nake ji dake nima ☺ kina sakamu nishadi Da Littafin ki 💞💦💞ILLAR BASHI💦💞💦 🤣🤣🤣 Ni ban taba jin irin wannan gidan sunan ba hatta ruwan da za'a sha ma bashi mai ruwan ya zuba 🤣 Dan akuya za'a yanka shima bashi 🤣 Abincin gidan bashi🤣 Kayan miya bashi🤣 Ba beauty bama koni bazan tsaya ba 🤷🏻‍♂🙇🏻


Kina wuta ina binki da fetur yar kanwata 😜Allah dai ya kara basira```




FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----






         *KARSHEN PAGEN BAYA*

Mukhtar ganin kowa yayi shiru shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani mugun kallo mai tsoratarwa. Ya shiga basu labari

» Ya fara da cewa Kimanin Shekara daya da rabi baya da suka wuce, lokacin ba'a fi watani uku da yin aure na da Ummiey ba. Lokaci ne da na shiga mawuyacin hali talauci ya min dankar kazar uwar ba'u. Ba komai ne ya kara zafin talaucin ba sai matsalar da muka samu da ogan gare jin mu na bar aiki. 




Nayi buga-buga na shiga na fita domin in sama abun yi amma abun yaci tura, duk inda na nema aiki bana samun aiki. Ranar wata laraba da naga abinci sakawa a baki ma yana shirin gagarar mu, Hakan tasa na shirya na dauki gatari na nufi jeji domin nayo itace na sayar. Hanya nabi ina tafe ina tunanin yanda rayuwa duniya tamin tutsun jaki lokaci guda na surmiyo kasa. 

 Rashin sa'a na ya tsananta ni kam bansa yama zanyi ba domin ko faskaran ban iya ba.

Naje ratsa wata fadama naji kamar maganar mutane a cikin wani dan lungu ina lekawa naga wasu yara ne guda biyu na dan tsorata da ganinsu kamar yanda suma suka frigita yarinyar ta kankame na mijin wanda ya kasance yayanta ne. Bayan yan tambayoyi da nayi musu suka bani amsa nan na dan saki jiki da su. Nace su fito muka sama waje muka zauna na tambaye su me sukeyi a nan. Namijin ne ya kalli kanwarsa hade da cewa "Rasheda in fada mishi". maganar da Yarinya tayi ya tabbatar min da yarinya ce mai wayo da hankali. "Eh yaya na ganshi da manyan kaya ina ganin kamar mutumin kirki ne ba irin su kawu mansur ba". Yaron yace "To amma amana". Na kallesa nace mishi "yaro ka yarda dani bazan cuce ku ba. Saidai ma in taimaka muku".

Kwarai a lokacin da tausayin su a raina.




Yaron ya shiga bani labari kamar haka: Yace mahaifinsa mai kudi ne duk anguwar babu kamarsa a dukiya. Yana da kani daya yaya daya. kawu abba da kuma kawu Mansur kawo abba shine karame wato kanin babanmu saurayi ne kuma shi mutum ne mai tausayi sabanin kawu mansur wato yayan su shida baban mu. Kawu abba yana san mu sosai mun shaku da shi sosai dake a gidan mu yake da zama shima yana da dakinsa daban. Hatta makaranta shi yake kai mu.

Ranar wata alhamishi ce mun dawo daga school muka tarar da abban mu da kuma kawu mansur suna rikici cacar baki abun kamar a buga. bamu san me ya hada su ba, koda ganin mu sai kawu mansur ya nufo hanyar fita wajen har ya kusan zuwa kofa ya juyo yayi bakaken maganganu hade da barazana wa baban mu, sannan ya fice baban mu yaji haushi sosai domin a lokacin daki ya shiga ya rufo. Kawu abba kuwa yaje yana tambayar maman mu ta fada mishi abunda ya faru amma taki gaya sai dai itama zubda hawaye take. 



Da da dare.

Har wajen karfe sha daya baban mu baiyi barci ba domin kuwa yasan halin dan uwan nasa zai iya turo mishi barayi su kwashe kudin kamar yanda ya fada. Kudin wasu filayan sa ne guda biyu ya sayar million biyu da rabi shine kawu mansur yazo ya tsare shi wai sai ya bashi million daya yaja jari. Shi kuwa baban mu yace yayi hakuri ba yanzu ba yanzu akwai abunda zaiyi da kudin. Shine abunda ya faru har kawu mansur yaji haushi ya hau fada harda barazana. 




Karfe 12:30am da yaji shiru-shiru ya kwanta a tunaninsa dama barazana ce kawai. Bai dade da kwanciya bq yaji hayaniya a kofar gida kuma kamar muryan mai gadi can kuma sai yaji ya kwala wani ihu! Wanda ya shaida mishi ba lafiya ba. Cikin sauri ya dauki jakar kudin ya nufi dakin kawu abba wanda muma a can muke a kwance. Bayan ya tayar da mu ya bawa kawu abba jakar kudin yace mu gudu ta kofar baya ga barayi nan sun zo wai shi zai tsaya in suka zo yace kudin basa a tare da shi.  




Kawu abba yayi juyin duniyar nan a kan baban mu ya taso ummanmu mu gudu tare amma yaki. Jin ana bubuga kofar palo ana neman ballata a shigo yasa ya ja hannun kawu abba har bakin kofar baya ya bude muna muka shiga nan fa muka bude yar kofar muka hau gudu. Bamuyi nisa ba mukayi yo wani ihu wanda muka tabbata na baban mu ne. kawu abba ya mika min jakar yace mu shiga wani dan lungun mu buya bari yaje ya gano. Haka kuwa akayi muka shiga wani dan guri mai duhu muka boye shi kuma ya koma, ko da shigarsa palo sai ya tarar an kashe baban mu da maman mu 'yan daban suna ganinshi sukayi chaf da shi suna cewa ga wanda aka bawa ajiyar kudin. 



Baban cikin su wani kato ne baki mumuna fuskarsa kadai abar tsoro ce. Shine ya tambayi kawu abba cikin tsawo ya fada mishi ina kudi amma yaki. Nan fa suka hau bugo naushin sa da mangarar sa. Hada masu yankarsa da dai yaga zasu kashe shi sai ya tsaida su yace zai fada. Nan take ya shaida musu kudin na wajen mu kuma ya nuna musu hanyar da muka bi. Koda gama nuna musu sai ogan barayin nan yasa hannu biyu ya murde wa kawu abba kai nan ya fadi matacce, su kuwa suka biyo hanya neman mu.

Tun daga nesa na hange su sun nufo hanyar da torch a hannunsu suna ha haskawa da dai naga in suka iso gare mu ba shakka sai sun gan mu. Nan take na kama hannun kanwata na dauki jakar muka ruga a guje. Har mun danyi nisa tukun suka hango mu. Suka kuwa rufa mana baya, tsabar gudu ban sani ba ta tsakiyar wasu masifafun karnuka na anguwar mu nabi. Ai kuwa suka hayayako har sun nufo mu kuma suka juya sakamkon jin gudun barayin nan. Nan muka barsu suna fama da karnuka inda mu kuma muka tsero fada mar nan yau kwana biyar kenan da faruwar haka in mukaji yunwa sai in dauki kudi in shiga gari in sayo mana abinci.

Wata doguwar ajiyar zuciya nayi da jin labarin yaron nan. Nace "masa yanzu ina kudin?". "Zan dauko maka ne kawai domin na yarda da kai ina ganin tausayi a idan ka kamar bazaka cuce mu ba". A cewar yaron, kallonsa nayi nace "gaskiya ka fada yaro ni ba kamar kawun ku mansur bane ku dauke ni kamar kawun ku abba". Nan take yaron ya tashi yaje ya daga wasu ciyayi ya fido katuwar jakar ya kawo gabana ya ajiye. Kwata-kwata yarinyar bazata haura shekara 8 ba shi kuwa babban namijin zaikai shekara 13 ko sama da haka.  




Koda ya kawo jakar gabana ya bude naga makudan kudin dake ciki kudin da ban taba ganin masu yawansu ba a duk tsawan rayuwata. Nan take naji zuciyata ta canza daga tausayi ya zuwa rashinsa zuciyoyi suka fara aikin bani shawar wari wasu na cewa in kashe yaran nan in mallaki kudaden wata zuciyar kuwa na cewa in dauke su in kaisu gidana. Daga karshe dai na aminta da shawara ta farko wato in kashe sun nan kuma na fara tunanin hanyar da zan bi dan kashe su. Sai kuma na tuna a kusa da ruwa fa muke, banyi wata-wata ba nasa kotar gatari na na bigi kan yaron domin nasan shine zaifi bani matsala nan take ya fadi kasa matacce, da ganin haka sai yarinyar ta fara ihu! Ni kuwa ganin zata tona min asiri na shake wuyanta har ta langabe gaba dayansu na kwashe su na zuba a wani ruwa dake wucewa ta tsakiyar fadama. Ruwan yaja su ya tafi da su, ni kuwa na dauko kudin na dawo gida nayi karyar cewa gonar mu na sayar mutane kuwa ciki harda matata da babanta gashi suka aminta sukayi farin ciki. Ba'a dade ba na bude shago na kama sana'a dan gudun kar kudin su kare. Ko da ganin na sama wannan kudi sai na shiga sabuwar rayuwa wato ta rashin mutunci bana ragawa kowa kuma bana san kowa ya raga min watta matata taga canji sosai a tare dani, ko ta bangaren addini na samu tawaya domin ko makaranta daina zuwa nayi wannan shine abunda ya faru inji Mukhtar.



"Innalilahi wa'inailaihir raji'un". Wannan kalmar ce take fita a bakin Ummiey da kuma mahaifinta. Nan da nan ummiy ta fara kuka tana fadin "Mukhtar haka kake dama ashe zaka iya kashe mutum ashe ba iyakar rashin mutun cin kawai kake da shi ba harda rashin imani?". Haka ta jero mishi wadan nan tagwayen tambayoyin wanda shi kanshi baisan wace kalar amsa zai bata ba sai kawai hawaye dake fita a idanunsa da gani kasan yayi nadama. Ummiey zata daga baki tayi magana abbanta ya dakatar da ita. Lokacin aljanar tace ina zuwa.  



Bat! Ta bace lokaci daya kuma sai gata ta dawo ita da wata yarinya wacce da gani a galabaice take tana cikin kunci da tsadar rayuwa kaysn jikinta kadai zasu fada maka hakan. Koda yarinya da aka kawo mai suna maryam taga Muktar sai ta fashe da kuka ta tashi ta ruga a guje, har ta kusa kai bakin kofa aljanar nan ta mika hannunta wanda a nan take ya kara tsawo ya kamo maryam dake shirin guduwa. Koda ji an sakalota sai ta fara kokarin kwacewa tana fadar "Shine ya kashe yaya sadiq dan allah karku bari ya kashe ni, macuci ne". 



Aljanar tace kwantar da hankalinki kawata ba abunda zai miki tsaya baya na. Mukhtar yayi matukar girgiza da ganin maryam wanda shi a tunaninsa saida ya kasheta tukun ya Jefata ruwa. "Wannan itace yarinyar da Mukhtar ya kashe yayan ta kuma yayi yunkurin kashe ta itama amma allah baiyi ba. Ta kubuta da rayuwarta daga mutuwa wanda ta fada wata rayuwar kuma wacce gwarama mutuwar da ita. Wannan yarinyar da kake gani fadamar nan ta koma mata gida duk sanyi duk zafi a nan take da safe take shigowa gari ta nemi abincin da zataci da dadare kuma ta koma fadama. Kwana uku baya nazo wucewa na ganta ana mata tamkar yanda kamin wato taje neman taimako ya bata abinda zataci ya kore ta. Ta koma gefe zauna tana kuka saboda tsabar yunwar da take ji dan duk ranar bata sa komai a bakinta ba. Koda naga haka sai na rikida zuwa tsohuwa na kai mata abinci bayan taci ne nake tambayarta ina iyayenta nan ne ta bani labarin duk abunda ya faru. Kaji irin tsadar rayuwar da ka jefata kai kuwa ka shiga farinciki. Mukhtar hukuncin da na yanke biyu ne ciki ka zabi daya....………………………





Aikin ki na kyau aljanar fatima.



Mujee zuwa.



Autan writers nee king boy










👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 9-10



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽




_Wannan pagen duk girmansa na masoya king ne a duk inda kuke._


💃🏻 *Kowa ni yake jira to gani na iso, Samari yan mata na nesa ku marmatso. Domin kar ayi babu ku haka sam! Sam! Bani so. Wannan pagen ku ne karku bari ya wuce wanda aka baya nan bai more kallo ba* 💃🏻😜


😍 wayyo my fans you will kille me with you love. Ina sanku ina alfahari daku *ANA TARE* supports 😘🤝



FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----






         *KARSHEN PAGEN BAYA*

Kaji irin tsadar rayuwar da ka jefata kai kuwa ka shiga farinciki. Mukhtar hukuncin da na yanke biyu ne ciki ka zabi daya.» Mukhtar ko dai ka mayarwa da yarinyar nan dokiyar ta ta hanyar bata duk wani abu da ka mallaka ta sanadiyar dukiyar su, ko kuwa ka zame mata ahali kamar yanda ka rabata da yayanta a baya, Dole ka bata kulawa kamar wacce zaka bawa diyarka ko kuma ma tafi haka. Domin da bazarta kake rawa. 





Malam ya kalli aljanar yace "lalai wannan hukunci yayi duk mai adalci haka zai yi, saboda haka ni na aminta Mukhtar sai ka zaba daya kodai ka tatara duk abunda ka mallaka hatta gidan nan dan da a gidan haya kake ka mayar mata ko kuwa ka rikr ta zabi ya rage ga mai shiga rijiya ko ya shiga ta kai ko ya shiga ta kafa. Mukhtar yace na aminta da zabi na biyun zan riketa amana isha'allah domin ni yanzu NAYI NADAMA sannan zan ci gaba da rokon allah ya yafe min laifukan da nayi, Kuma na gode wa wannan aljana da ta tsamo ni daga cikin halaka. Maryam zo mana daga yau kin zama 'yata". Ya mika mata hannu da farko taki amincewa saida aljanar tasaka baki tukun. 




Ummiey farin ciki tuni ya mamaye ta jin ta sama 'ya a bagas! Ta sama mai maye mata gurbin yarta hawwer da ta mutu. Aljanar ce ta wani tashi saman iska gaba daya iskan wajen ya hau zagaya ta ita kuwa ta fara wata kalar shu'umar dariya marar dadin saurare, Magana ta fara yi muryar na fitowa uku-uku bazaka iya banbance namiji ne ke maganar ba ko mace ko kuwa yarinya. "Nice nan aljana SUFURATU marainiyar aljana, Sai na cika burina na ganin ba maraya da zai kasance a cikin kunci. Aikin ma yanzu na fara. Sannan Mukhtar ina gargadin ka a kan maryam kuma ka zama mai adalci domin zan dinga bibiyar rayuwar ku". 




Sama tayi kamar wacce ake ja tana tafe tana gagaba dariya, su kuwa da gaba daya in aka fitar da malam ba wanda bai tsorata ba, domin ummiey har dan fitsari ne ya fara kubice mata. Tun suna ganinta har ta bace cikin gajimare. Malam ya kara yiwa Mukhtar nasiha sannan ya bashi addu'o'i wanda zai tuba ga allah ya kara da cewa ya yawaita sadaka, tukun ya musu bankwana ya koma. Su Mukhtar sunga abun mamaki yau kam duk cikin su ba wanda tsoro ya sake shi, nan fa aka shiga tarairaya da tattalin maryam dan gani suke kamar itace ma aljanar. 





Acan gidan kamala kuwa da asuba da suka farka sama ko kasa suka nema yarinya suka rasa sun shiga rudu da tashin hankali don har ga Allah yarinyar ta shiga ransu fiye da zato, a cikin su ba wanda baiyi mafarkinta ba. Khadija ta zauna tayi zugum ba abunda take sai faman kuka tana tuna yarinyar nan da irin shakuwar da ta shiga tsakanin su tun a jiya. Yau komi bata iya ci ba har wajen karfe 9:00 ta zauna ne kawai ta zurawa kofa ido a zatanta zataga ta shigo. Kamal da yaga abun yayi yawa yayi lalashin amma kamar kara haukatata ne yake. "Khadija tunda kinki hakura tashi muje nemanta". Firgigit ta tashi da gudu ta shiga ta dauko hijab. Sun taho sai sauri take tana leke-leke wani wajen ma har gidaje take tatan bayawa. Amma har wajen 11 babu labari. Duk sun gaji sunyi tikilis. Sufuratu tazo wucewa ta hange su a karkashin wata inuwar mangwaro da sauri ta sauko kasa tazo daidai inda suke, ita har tama manta da su, "Allah sarki da gani nemana kuke na gode da halacin da kuka min bazan taba mantawa da ku ba. Badan aikin dake gaban Sufuratu nada yawa ba da ba makawa DAKE ZAN ZAUNA".duk abunda take fada baji ba suke kuma basa ganinnta. Kwasar su tayi ciki abun da baifi seconds 5 ba ta kaisu gida. Mamaki iya mamaki sunyi shi ya akayi hakan ta faru mu da muke tsaye a gindin bishiya kuma gamu a gida. Tambayar dake dauke a bakin ko wannan su kenan. 





"Na tafi sai mun sake haduwa" gaba daya sunji an fadi wannan saidai basu san taka mai-mai ta inda muryan ta fito ba. Nan fa suka shiga dube-dube. Aljana Sufuratu kenan yarinya ce a cikin aljanun ma domin da kadan zata haura shekara 150 musulmar aljanace labarin ta nada dan tsayi da abunda yasa ta fara taimakon marayu. Kasan cewar itama yarinya ce yasa tafi shiga rayuwar yara marayu, dan a ganinta sunfi ban tausayi. Indai taga yarinya cikin wahala saita bibiya rayuwarta ta kuma san labarinta. A yanzu haka ta bar garin abuja ta nufi bauchi.  




Inda ta sauka a G.R.A anguwar masu kudi ce, kowa harkar gabansa yake yi tankama-tankaman gidaje ne tsabar rana da akeyi yasa kowa yana cikin gidansa. A farkon anguwar Safuratu tayi gamo da abunda ya bata mamaki wata yar digil gilar yarinya ce karama wace in tayi gudu takai 10 years ko 9 da rabi. Sanye take da kaya atamfa dinkin riga da sket sun mata kyau sosai da gani kasan ba yar talaka bace. Kanta wani dan bokitin ruwa ne wanda da gani kasan yafi karfinta jan haline kawai yasa take dauke da shi sai jibi take da alamun gajiya a tare da ita daga nesa ta debo shi. Ba wani abu yabawa Safuratu mamaki ba sai ganin gari da wuta kuma zaiyi wuya a sama gidan da ba tanki a anguwar. Hakan yasa tace a ranta bari ta bita sai taga wace marar mutun cin uwace wannan, da take neman hallaka diyarta.   




 kofar wani gida ta kalla nan take ta saki murmushi, da kyar ta samu ta sauke ruwan ta ruga da gudu kofar gidan nan wata yar baby ce (Diyar roba ta dauka) nan fa ta sama waje ta zauna ta fara wasa da ita ta bar ruwan da ta dauko din kan titi, dake motoci basa wucewa. "Kutumelesi lalai fatima yau kuwa zaki daku wato har kin sama damar taba yar babyn nuratu ko". Kafin ta juyo tuni yarinyar dake maganar ta warce yar babyn hade da kifa mata mari wanda saida ta gigice. Kuka ta farayi Wiiii!-Wiii ta juye ta kalli wacce ta mare ta din tace "Wllh sai na gayawa mama asiya". "Jeki ki fada din kiyi sauri kar kuda ya riga ki". Cewar mai marin,




Fatimar bata kara cewa komai faman kuka da take ga hawaye ga jibi abun yayi mata biyu. Zuwa tayi taje ta fara kikiniyar dora bokiti a kai,Da kadan ta fadi ita da ruwan badan Safuratu tayi sauri ta tallafa mata ba. Dungwai-Dungwai ta hau titi ta tafi tana kugin kuka. a bakin wani makeken gida ta tsaya tana kwalla kira "Me gadi bude-me gadi". Aljana safuratu dake binta a baya ta tsaya ta kare wa gidan kallo tas! Taga a duk anguwar gida daya ne za'ace sunzo daya da wannan gidan ta girman shi da kyawan shi, da gani kasan an kashe nera, "To ke kuwa me zakiyi a nan gidan ko wata sabuwar tsokanar ce domin bana tunanin yar nan gidan ce ke". Safuratu ke magana ita kadai. Mai gadi ne ya taso da sauri yana masifa "Ke ki tsaya inzo in bude mana kin ishi mutane da kira". Bayan ya bude ya gallah mata harara wa kuma ya tabaki kika zo kina bude mana baki?". "Zulaihat ce ta mare ni". Ta fada lokacin da ta wuce ciki, "Dan an dan mare ki shine zaki ishe mu da kuka kuma, yarinyar nan dai anyi ja'ira". 




Tun a kofar falo ta fara kira "Aunty ameera-aunty ameera". Da sauri ta fito tana mata masifa to jarababa kin dawo wato har kinzo kin fara takurawa mutane". Ameerar ke fada haka lokacin da ta sauke mata ruwan tana juyewa. Hanyar daki ta nufa da sauri ta kamota, ubanki nace Fatima dan iskanci ina zaki?. Ko kina nufin wannan ruwan ne zai ishe ni wanki?". "Aunty zuwa zanyi in gayawa mama asiya Zulaihat ta mare ni". Ta fada tana shashekar kuka "Muna fuka ai ba'a banxa zata mare ki ba da abunda kika mata, oya ni wuce ki karo min ruwa wllh sai kinyi sawo uku nan gaba". Rushewa tayi da kuka "wllh ni dai na gaji wajen yayi nisa aunty ki tausaya min ki deba a can". Wani tankin ruwa ne ta nuna da yatsarta ya cika sai zuba yake ma. A lokacin Safuratu ta gane cewa ba rashin ruwa yasa aka tura fatimar ba mugunta ne kawai. 





 "Kan uba! Iyee fatima ni zaki dinga fadawa kin gaji in aike ki kice kin gaji?". Kwashe ta da mari tayi dan karfin marin har saida ta kusan faduwa. Wani sabon kukan ta dora dashi mai karfi. Da gudu naga wata budurwar ta fito daga falo tazo ta kama fatima tana kalan waccan, "Haba ameera wai miyasa ke muguwa ce bakya jin tausayin yarinyar nan ko kadan shin so kike ki kashe ta ne?. Kin turata debo ruwa dan iyayi bayan ga ruwa nan yanzu kuma kina dakar ta gaskiya karki kara dukanta".  




"An daka din kiyi abunda zaki yi bari ma ki gani inci ubanta a gaban ki inga ubanda ya isa ya hanani". Fatimar ta nufa ta daga hannu zata kara marinta da sauri Wacce ake kira Iddau charaf! ta rike hannun, "Ameera wllh bazaki dake ta ba a kan me wato ita batada gata ko?". Ameera tace, "Sake min hannu, sakar min hannu". "Anki a saki ki kwace in kina da karfi". Haba wa ai kafi ta rufe baki tuni Ameera tayi kukan kura ta chakume ta, nan fa suka hau kunce harda naushe-naushe. Safuratu na tsaye tana kallan ikon allah abun ya fara rikitata.



 Wasu yan mata ne a daki su biyu kusan kansu daya da kadan dayar ta dara daya Zan iya cewa daya shekarar ta 12 dayar kuma 14. Daga ganin su kaga mararsa jin magana ta kwaliyar da sukayi ma kadai ta isa ta sheda maka hakan ba kauya wa day ba wannan kwaliyar taci uwar ta kauyawa day a hauka. Kamar ance wa mai suna Asma'u ta kallo waje ta window. Wani dan kara tayi na jin dadi nan da nan ta mike.Yawa bigi ciki aunty ameera, karki bari ta kada ki aunty iddau". (fiddausi suke kira da iddau) koda jin haka naga dayar ta bar abunda take da gudu tazo ta haye kan gadon itama ta fara leke. Tsalle tsalle suke suna dunkule hannu suna fadin bamu rabawa saidai mu kara zugawa bigi cikin dan bari bakin. Maganar da suke tana kaiwa har kunnuwan masu fadan amma basu bari ba sai ma kowacce ta kara dadagewa. Su kuwa su Asma'u komawa sukayi Kamar dai supports a filin Wrestling ko wacce ta zaba wacce take so............



Mujee zuwa.



Autan writers nee king boy














👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 11-12



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽



😍😽 *IN DEDICATION TO YOU OUR NASMAT* _Ina ji dake wllh in kikayi fushi dani ina zan saka kaina 😪 Da bazarku nake rawa ZAMANI You're my blood body Au!_ 🙊🤣


😍 I love you all my fans 💃🏻


Even if you haven’t found your love yet, don’t worry, with time comes a lover! 😍😘



```FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----```






*Afuwan Readers nayi amfani da SUFURATU Maimako SAFURATU a farkon pagen baya.*





        *KARSHEN PAGEN BAYA*

Maganar da suke tana kaiwa har kunnuwan masu fadan amma basu bari ba sai ma kowacce ta kara dadagewa. Su kuwa su Asma'u komawa sukayi Kamar dai supports a filin Wrestling ko wacce ta zaba wacce take so...»Wata mata ce mai jikin sosai da gudu ta fito tana "kai kai ku bari mana" Da kyar ta samu ta raba su a cikin su kowacce taji jiki. Sai Huci suke suna hararen juna. "Me ya hadaku kuke fada ku da kullum bakwa rabo da rigima kamar Ba yan uwa ba". "Momy wai dan na daki waccan shegiyar yarinyar shine tazo wai zata rama mata". Ameera ta fada tare da nuna Fatima dake tsaye gefe tana hawaye. Harara matar ta galla mata tare cewa "muna fuka ai kinga ta koma gefe tana hawayen munafurci, ke kuma Fiddausi wllh hawainiyarki ta kiyayi ramata, in badan iskanci ba saboda ta dake wannan Yarinyar zaku kama fada da yar uwarki".



Asama'u da Nasima (Suke kira da nasmat) Ba karamin haushi sukaji ba ganin mama asiya taje ta raba fadan. Mtseewwww! A tare suka ja tsaki, "Wannan mama Asiyar gaskiya mu dai bata gyara mana ba wallahi allah ya isa". Cewar Nasmat. Asma'u taja tsaki mtswww!, "Ni har ta bani mugun haushi wallahi Duk da tana momy na. ta wani taho tubur-tubur da ita kamar kaza buloras irin lutayan nan kinsan fa basa iya tafiya sosai in suka girma bari kiga irin tafiyar maman mu". 



Nan fa Asmart ta sakko ta fara nuna kalar tafiyar, harda irin Dafe kugu yanda yan lukutaye suke in sun gaji. Da sauri nasmat ta sakko "dallah malama ba haka take ba bari kiga ni". Itama kwakwayan tafiyar mama asiya ta shiga yi. Bayan tayi tafiya mai dan tsayi Asmart na tsaye na kallo da gudu ta dawo tana fadar "kuma bari kiga yanda take in taci ta koshi ta kasa tashi daga kwance". Kwantawa tayi Rairan a kan katifa tukun ta fara wani jujuyawa tana irin juyin nan da karfi abun in kagani dole kayi dariya. Asmary ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya. Daga bisani kuma ta dan tabe fuska alamun tayi fushi. Kulli ta kaiwa asmart a baya "Dan ubanki ki bari mamana ne fa". Asmart ta mike tsaye dariya ta kusan kubuce mata, matawa nayi kuma ai ke kika fara. Gaba daya suka saki dariya har suna rike ciki kamar mahaukata.



Fiddausi ta tace "Haba mama asiya ya za'ayi.....". Tun kafin ta idasa maganar mama asiya ta daka mata tsawa "Ke rufe min baki wallahi ko in gwab gwabje ki yanzu a gurin nan, marar kunya" Fiddausi tafiya tayi tana bubuga kafa tana gunguni. "Ke me kike cewa. Zagina kike ko?". "Ni dai bance komai ba". Kunnan fatima mama asiya ta kamo hade da jawota gabanta. "Munafuka ke kuma zo nan uwar iyayi, wato dan an dan bige ki ne kike wa motane kuka ko, to na kori mai rama mikin muga kuma uban da zai ramamiki yanzu".  




Dankwashin ta tayi a kai hade da cewa "Ameera gata nan ki mata abunda kike so inga wanda ya isa ya hana ki ko uwarta tazo nan bata isa ba balle ma tuni ta bar duniyar". Tana gama fadar haka ta tura Fatima ta fada jikin Ameera ita kuwa ta koma falo. Koda jin mama asiya ta fadi haka Sai ran Safuratu yayi mugun bace tuni idanunta soka koma jajur kamar garwashi, "Wato.marainiya ce shiyasa kuke gana mata azaba ko to kunyi na karshe". A cewar Aljana Safuratu tana maganar ne a kusa da su amma su ko kadan basa ji. 




Ameera ta dauki bokitin ruwa ta kara dorawa Fatima a kai maza wuce ki debo min Ruwa wllh sai kinyi sawu uku ko mutuwa zakiyk ba kuka ba". Fatima tana kuka abun tausayi ta kama hanya ta koma debo ruwa, bayan taje ta debo a gajiye ta kawo amira ta juye ta kara bata bokitin wai ta koma. Fatima ta fashe da wani kukan domin ji take kafafunta kamar zasu tsinke dan gajiya, amma ba yanda ta iya dolenta ta karba ta tafi tana tagal-tagal mai gadi shi kanshi ya gaji da bude mata kofa, tuni ta bata mishi rai shi ba abun ya bigeta ba yayi ta aikinsa domin yasan yanda take a gun alhaji Fatima na tafiya a gajiye jiri ya fara debarta nan take ta fadi kasa a galabaice. (Wayyo Rashin uwa)  




Wani alhaji ne yake tafe a cikin wata dan kareriyar mota tun daga nesa da ya hange ta ya fara cewa "Wa nake gani haka kamar mama ta?. Bai tabbatar da itace ba saida ta tafi faduwa, ai kuwa yana ganin ta fadi ya danno motar kamar wanda zai tashi sama dan tsabar gudu. Aljana Safuratu tayi niyar taimakawa fati kenan taga motar nan ta dirfafo gare su hakan yasa ta koma gefe. 




Wani mugun birki yaja ji kake kiiii! Kafin motar ta karasa tsayawa ya fara kokarin fitowa. "Mamana! Mamana!" (Sunan da yake kiranta da shi kenan dan sunan kanwar mahaifiyarsa kenan wacce ta rike shi)

Tashi mamana me ya same ki, da sauri ya dauke ta yasa ta a mota sai ma da zai shiga mota tukun ya hangi dan bokitin can a gefe Ya kuma dubi jikin fatima ya ganshi a jike "tabbdijam Lalai Asiya baki so zaman lafiya ba". Abunda ya fada kenan ya shiga motar ya fara tafiya. Sanyin AC ne ya farfado da Fatima daga yar guntuwar sumar da tayi.  



"Oyoyo dadyna Yanzu kazo?. Abunda ta fada kenan lokacin da ta kara matsawa jikinsa ta dan jingina da shi. "Mamana me ya sameki ne na ganki a nan a kwance kuma da bokiti kusa da ke ga jikinki a jike ina zaki?". Shiru tayi na dan lokaci tukun tace "Baba ruwa naje debowa zanyi wanka". Hararar da ya daka mata tasa tayi saurin cewa "Aa baba ba wanka ba wanki zanyi". Kalansa tayi taga ba annuri a fuskarsa nan take ta sake canza magana "Baba dama shukoki ne zanba ruwa basa san ruwan gidan mu". Tsawar da ya daka mata ta firgitata abunda abbanta bai taba mata ba kenan nan take ta fashe da kuka. Rai a bace yace, "Mamana ban sanki da karya ba karya ba halin mutanan kirki bane shin waya koya miki karya, in kuwa kika ce karya zaki dinga min to wllh kinji na rantse bazaki sake ganin hakoran dariyana ba". 


Cikin kuka tace,

"Dady kayi hakuri wallahi zan fada ma Aunty Ameera ce tace sai na debo mata ruwan wanki wannan sawuna na uku kenan gashi na gaji amma taki ta hakura ta barni in huta". "What! Yanzu duk kankartar ki ameera ta aike ki dauko ruwa?". Kai ta daga mishi "A ina kike dibo ruwan?, Su Asma'u basa gidan ne?". "A can wajen makarantar mu ne. Dady suna gidan mana a daki suke ma". 



"Innalilahi!". Ji yayi kamar ya fashe da kuka domin allah ya gani ko shi bazai iya sawu biyu ba daga gidansa zuwa can balle ma wai ace wannan yarinyar kuma harda ruwa a kai. Ranshi ne yayi mugun baci Fatima sai surutu take amma saidai ya kada mata kai dan ko maganar ji yake bazai iyaba.  




Da gudu ya karasa kofar gidan ko daga odar da yake ya isa kasan ya dau zafi, dan in kana kusa da shi sai ka rufe kunnuwa, da gudu mai gadi ya zo ya bude yana shiga ya parking din motar ya futo a fusace ya nufi Garzali mai gadi baisan hawa ba baisan sauka ba yaji saukar mari a kumcinsa. "Garzali ashe kai aikin banza ne ban sani ba ashe a banza nake biyanka kudina in wata yayi". Cikin murya mai rawa "Afuwan ranka ya dade bansan laifin me nayi ba". "Au bakama san miye laifinka ba ko uban wa yace ka budewa Fatima kofa yanzu in diyarka ce dan gidan ku zaka barta taje debo ruwa ne. To daga yau wllh in na sake kamaka da irin wannan laifin a bakin aikin ka". Fuuu!! Ya wuce kamar jirgi mai gadi ba abunda yake sai bada hakuri harda durkusawa a gun. Bayan alhaji ya danyi nisa ya tashi yace a kan wannan yar banzar yarinyar ana min barazana da aikina". "Me kake cewa?". Inji alhji "Aa Alhji cewa nayi ayi hakuri zan kiyaye".




Tun daga kofar falo ya fara kwala kira "Ameera! Ameera!". yana janye da hannun Fatima. Nan danan saiga ta ta fito Jikinta na rawa dan tasan abunda ta aikata ko kadan batayi tunanin abban nasu zai zo war haka ba. "Dady gaaa..". Saukar tagwayen mari da taji ne ya hanata idasa maganar sai ihuu! da ta kwada mai karfi! Kafin kace me falon ya kusan cika Da yara da manya bansan haka gidan nan keda iyalai da yawa ba sai yanzu. 




Asiya ce tazo ta rungume Ameera dake faman kuka. Alhaji ya fara magana. 

 "Ke dan ubanki baki da hankali ne ya za'ayi ki aiki wannan yarinyar wai ta debo miki ruwa har can wata uwa duniya baga kanan ki nan ba wanda suka fita me ya hanaki aike su ko zaluncine kawai abun, to wai ma inace dazun nan da aka kawo wuta Nasa aka kunna soma?". "Haba alhaji dubi fa yanda ka kunburawa yarinyar nan kumatu kamar dai ba yar uwarta ta aika ba, kawai fa uniform dinta ne zata wanke kasan farare ne shine fa ta aiki Fatima ta debo mata ruwa a can kasan yafi na nan haske". Asiya ce ke maganar lokacin da take lalashin yar tata. 



"Asiya! asia! Sau nawa na kira sunanki,.?". 3 Ta bada amsa a Hatsale, "To wllh asiya ki fita a idona zan miki rashin mutuncin da bakiyi zato ba wato duk ke kike daurewa yaran gidan nan gindi suke abunda suka ga dama ko?. To bari kiji in gaya miki wllh duk wanda yake so muyi zaman arziki da shi a gidan nan to karya ya taba mamana in kuwa mutun bai yarda ba ya gwada taba ta yaga abunda zai farubda shi". Yana gama fadar haka ya kama hannun Fatima ya nufi dakinsa. Ya fara tafiya kenan asiya ta fara gunguni kamar yarinya "Shikenan wato sai a raba kan yara a hana su shakuwa da juna". Maganarta ce tamai zafi sosai yaji bazai iya daurewa ba. Sakin hannun fatima yayi da gudu ya Nufe ta, Abunka da lukutar mata bata da gudu ta ruga amma baisha wuya ba wajen kamota. Koda yaje sai yasa kafa ya kwalfe ta nan ta fadi ta fara wash! Wash! Wayyo ya karya ni. Bai ko tsaya kallanta ba ya wuce ya dakinsa shida fati. 




Asmart da Nasmat ne suka kalli mama asiya tukun suka bushe da dariya ganin ta a kasa kamar an zaunar da buhun masara. Kowa na gurin abun ya bashi dariya har kishiyoyin nata guda biyu dake tsaye a gefe. Saidai kowa yasan jarabarta duk gidan dama ba wanda zai iya mata dariya sai wannan biyun marar ji. Ai kuwa kafin kace me ta yunkura da kyar ta tashi tubur-tubur ta nufe su wai da niyar ta kamosu ta daka, kafin kace me tuni sun ruga upstairs tana biye da su koda tahau matakala na daya biyu sai sulbi ya kwashe ta ji kake tum ta fado kasa kamar an yarda buhun masara. Kanta ne ya bugu da kasa. Su asmart da suka juyo sukaga abunda ya faru sai suka dora da wata sabuwar dariyar.................






Hmmmmm Gidan nan za'a sha kallo naga alama. 




Mujee zuwa.




Autan writers nee king boy


Comments