ALJANAR FATIMA 1 TO 6 Hausa Novels

 


👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Part 1-2



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽



*بسم الله الر حمن الر حيم*



 _*YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MAMALAKIN KOMI DA KOWA WANDA YA DAI-DAI TA GABOBINA*_ 


 _*TSIRA AMINCI KA DADAWA FIYAYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD S.A.W SHUGABAN HALITTA CIKA MAKON ANNABAWA*_



 _*INA ROKON ALLAH A KAN RUBUTUN NAN DA ZAN FARA ALLAH KA IYA MINI KA BANI KAIFIN BASIRA DA HIKIMA ALLAH KASA NA RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANE MU DUNIYA DA LAHIRA, AMIN.*_




💃🏻 GA WATA SABOWA ZAMANI MAI YAYI SABUWA. 


Bazan manta da ku ba domin kun zama My blood. 


Bazan barku ba domin in na barku na bar kaina.


Bazan ki yaban ku ba domin yaban gwani ya zama dole.



Bazan hana ku ba dole in mika shi gare ku littafin baki daya sadaukarwa ne gare ku MY BLOOD duk yan Kungiyar Zamani writers association ®Z.W.A banga kamar ku ba bakwa taba nuna banbanci 

❤😍






💃🏻 ```Bazan taba mantawa da ku ba masoyana a duk inda kuke alherin allah ya kai muku kuna a heat na.


Bari in fara rubuto ku🤦🏻‍♂ Kash! Nawan in na fara rubuta ku bazan idasaba har karshen littafin ga ruwa biro na kadan ne. Ilove you my fans```




A Cikin kado anguwar hausawa dake babban birnin tarayya Abuja.anguwa ce mai lunguna gata da tarin bishiyoyin mangorori hankan ne yasa anguwar take da inuwoyi hakan ta haifar wa da wajen duhu dan daga ance ma karfe 6 tayi to sai an haska fitila tsabar duhu in dai ba farin wata ba. Anguwa ce mai tarin jama'a, ko ta ina ka duba mutane ne kowa na uzurinsa. Akwai masu saide-saide da yan shaguna da irin tsofafin nan masu saida kayan makulace na yara. 




Wata yarinya ce sanye da doguwar farar riga wacce ta koma baka dan tsabar datti, Yarinyar fara ce kallo daya zakayi mata ka gane hakan saidai dauda ta masheta baka. Gashin kanta mai tsayo ne amma rashin gyara yasa duk ya fara cicirewa tsabar datti gashi duk ya barbaje mata a fuska sai ta dage shi tukun take iya ganin gabanta.  




Duk mai tausayi yaga yarinya to dole tausayinsa ya lunku a kanta. Domin tayi kalar ban tausan. A hanakali take tafiya har ta isa bakin kofar wani shagon saide-saide. Bakin kofar shagon taje tayi tsaye ta dan yace gashin da ya lilube mata fuska tana kallan cikin shagon. Shi kuwa mai shagon a lokacin ya dan duka daukar wani abu. 'Da dagowar shi duka hada ido da ita sai ji yayi gabansa yayi mugun faduwa.




Nana take yanayinsa ya canza kalo daya zaka mishi ka gane ya fusata ainun!, "Ke uban me zan baki iyee?, haka jiya ma kika zo kika min tsaye a kofar shago kina wani nuna min ciki da baki, gaki yau kin kuma Dawowo uban me zan miki". 



Dayan hannuta ta daga ta dage baki hade da nuna yatsar ta cikin bakin tukun ta sauke shi ta nuna cikin ta kamar dai yanda tayi mishi jiya. Wanda duk me hankali in ya gani zai gane tana nufin yunwa take ji tana bukatar abinci, Shima kuma kanshi ya fahimci hakan. 




"Kaji rainin wayo ah! Lalai wannan baki sanni bane baki san bani da mutun ci ba to wllh yau zan nuna miki, to ni ubanki ne da zaki ringa nuna min kina jin yunwa ko dan kinga jiya korar ki kawai nayi ban taba lafiyar jikin ki ba. Bari ki gani".

Nan take ya juya ya dauko dorina mai baki biyu wacce take jike dai mai dan tayi zafi yasa ta a mankyada Dama saboda yara ya saye ta. Goge bulalar ya fara yi domin abun man har yanzu akwai maski duk abun nan da yake yi yake yana surutai. Wato baki san na dade banyi zalinci ba ko ni dama zalinci ai rigata ce in banyi shi ba ji nake kamar a zigidir nake". Juyowa yayi a zatansa tuni taji tsoro ta gudu ganin ya dauko bulala, amma sai yaga sabanin haka ta sake bude baki ta nuna mishi kamar yanda tayi dazun. 




Kara fusata yayi da sauri ya bude yar karamar kofar ta kata ko ya fito. Baiyi wata-wata ba ya fara tsula mata bulala harda riketa yana fadin, "Bari in zane ki tukun gobe ma ai sai ki dawo kaji jarababiyar yarinya ni da ba ubanki ba taya zan baki abinci" yana yi ne yana dukanta tun tana kuka a hankali har ta fara ihu! Abunda da ya jawo hankalin mutane makwabtan shagon sa kenan. Sukayo mishi can aka kwaci yarinyar shi kuwa sai masifa yake. Wai ta rainashi gobe ma ta dawo. 




Wani dan saurayi ne naga ya kama Yarinyar yana lalashita bai ko ji kyamar ta ba kamar yanda sauran mutanan gurin sukayi. "Yi shiru yi hakuri yarinya kinji. Haba muktar yanzu dama rashin mutuncin naka har ya kai ga haka ban sani ba?, Ai da na dauka rashin mutuncin ka da masifar bai wuce iya manya ba ashe hada yara". A cewar wanda ya kama yarinyar yana lalashi.


"Eh kamalu da ba ka sani ba kuma da ji kake yi yanzu kuma gashi ka gani da idanunka iyhee! Nayi rashin mutuncin in da yanda za'ayi dani ai sai ayi mugani". 

Da jin haka mutanan wajen suka watse suka barsu su biyu a gun domin kowa gudu yake ya wa Muktar magana ya mai rashin kunya, Dama a wajen kamala ne kadai baya raga mishi duk rashin mutuncin shi yana tsoran kamala.


 


"Kadai kaji kunya wallahi, yanzu wannan karamar yarinyar me tayi maka da ka dake ta?". 

Muktar ya wani taso da masifa kamar zai haiye kamal din, " Kai kamala ka bar ganin fa ina daga maka kafa wllh ba tsoranka nake ji ba, ya za'a yi kazo kana min maganganun banza a kan wata yarinya wacce gata nan dai kamar ma yar mahaukaciya domin wannan tafi karfin ace mata ma almajira, kawai tazo kofar shagona tana daga min baki wai yunwa jiya na koreta yauma shine ta dawo shiyasa zan zane ta gobe ma in ta dawo haka sai na zane ta". Yana gama fadar haka bai ko tsaya sauraren kamal ba ya juya ya shiga shagon shi.

Kamal jin saboda ta nema abinci ne ya dake ta dan takaici bai sake cewa komai ba ya kama hannun yarinyar ya nufi gidansa da ita dake ba nisa daga nan. Yana rike da hannuntq tana binshi suka shiga gidan, matarsa Khadija tana shara a tsakar gida tana jin salamar shi ta mike tsaye tana kalanshi tana kuma kalan yarinyar. 




"Baby sannu da zuwa wannan fa daga ina". ta fada lokacin da take kokarin kama hannun yarinyar. Kamar rai a bace ya kwashe duk yanda akayi ya gayawa matarsa, khadija nada mutunci sosai nan take taji tausayin yarinyar da sonta a cikin ranta. Gogewa yarinyar hawaye tayi hade da cewa, "Yi hakuri kinji yan mata share hawayen ya sunanki daga ina kike". Wannan tagwayen tambayoyin ta jera mata, amma shiru yarinyar batayi magana ba sai ido da take binsu da shi. 




Kamal ya maimata tambayar kamar yanda matar tashi tayi amma shiru. Sun tambaye ta ya kai sau biyar amma ko umh! Bata ce ba sai idanu da take binsu da shi. "Baby inaga fa wannan yarinya kurma ce shi yasa ma bataw Muktar magana ba". 

"Kwarai nima nayi tunanin haka, yanzu abunda za'ayi ki taimaka ki mata wanka ki zuba mata abinci taci bari inje in sayo mata wata rigar ji kafarta ko takalmi babu bari in hado da shi". A cewar kamal domin yasan matarsa ba mai bijirewa umarninsa bane ko mi ya gindaya mata inda ba na sabawa allah bane tana iyakar kokarinta. 




"To baby a dawo lafiya". ta fada lokacin da ta mike shima kuma ya fita Kafin wani dan lokaci tuni khadija tayi wa yarinyar wanka ta wanke mata kai. Tsabar dauda saida ta bata kusan bokiti uku da mai tsantsami ce bazata iya ba domin ko ita tanayi tana dode hanci dan tsabar wari. Bayan ta gama wankan bata mayar mata da rigar ba wani zaninta ta dauko ta liliba mata tukun ta shigar da ita ta zuba mata abinci. Ita kuma kamar wanda ya shekara baici ba haka ta fara ci hannu baka hannu kwarya. Tana gama cin abincin sai ga kamala ya shigo da sabuwar riga da takalmi mai kyau. Ya kawo ya mikawa khadija yace "ki saka mata ni zan koma shago karki bari ta fita waje".  


To khadija ta ambata. Kamala ya kalli Yarinyar mamaki ne ya cika sa ganin irin kyawan da ke gare ta ashe dama tsabar datti ne. Baidai ce komai ba ya juya ya wuce.

Khadija ta shafawa yarinyar mai mai kanshi tukun tasa mata kaya. Ta kuma tatara gashin kanta wuri guda tasa ribbon dinta ta daure mata kan, ta jawo ledar ta bude taga ashe doguwar riga ce mai wando harda dan gyale. Ta saka mata tukun ta mikar da ita tsaye ta tsaya ta kare mata kallo sama da kasa. Wow× Masha allah beautiful baby kenan, yarinya da shegen kyau kamar aljana.


 (Nasmat tace, kaji min mata me ya kawo maganar aljana kuma a nan ko dai so kike ki tunawa king) 



Khadija tace "bari in saka miki jan baki da hoda kina so". Lokacin tama manta da yarinyar bata magana. Bisa mamaki sai taga Yarinyar na girgiza kai alamun eh. Dan dariya taye hade da cewa "dama kina jin magna ne bakya yi".   



Nan ma girgiza kai tayi alamun eh, Nan fa murna da farin ciki ya cika ta. Ta kuwa fara jero mata tambayoyi kala-kala. 




'Acikin tambayoyin ne ta tambayi ina ne gidan su ta nuna bata sani ba ta sake tambaya ina iyayanki nama ta nuna bata sani ba har da hawaye. Khadija ta shiga lalashi tace "daga yau na zama maman ki kin yarda". Girgiza kai tayi alamun eh 




Nan take khadija ta rungume ta cikin farin ciki domin allah ya zuba mata san yara kuma har yanzu allah bai bata haihuwa ba sau biyu ko ta sama cikin bari take. 


(😭 ayya allah sarki allah ka bawa duk mai irin wannan matsala haihuwa sister na allah ya kawo 👏🏽)




Haka dai ranar Khadija ta wuni cikin farin ciki duk ina tayi yarinyar na biye da ita tuni suka yi sabo har da wasanni a tsakanin su. Da magariba haka kamala ya dawo ya tarar da su khadija ta bashi labarin duk abunda ya faru ta gaya mishi ashe tana ji magana ce bata yi.  


Nana shima yayi mata mgana ta gyada kai. Kamala yace "To yanzu bata magana taya zamu san sunanta?".  


Khadijah tace "kaji wata matsalar kuma ni nama manta in tambaye ta tun dazun. (Ta juya wajen ta) kin iya rubutu". Yarinyar ta girgiza kai alamun a'a. Kamala yace "to mu saka mata suna waleeda mana tunda dai can dama muna san sunan". 




Khadija tayi murmushin jindadi ta kalle ta tace,"Kin yarda sunanki waleeda?". Da sauri ta girgiza kai alamun eh tana dariya nan fararen hakoranta suka bayyana.  





Bayyan isha'i sunci abinci sun suka danyi kallo kadan wajen karfe goma suka tashi ita kam yarinyar tuni tayi barci ma. Khadija ta dauke ta suka nufi daki suka kwanta a tskiya suka sakata khadija saida ta kare wa yarinyar kallo da kyau tayi murmushi tayi mata kiss haka shima kamala san yarinyar ya shiga zuciyar su lokaci guda. 





Khadija saida ta dora wa yarinyar hannu ta dan rungume ta tukun ta fara barci. 


Uhmmmmm wannan kenan😊

Misali karfe 11:00pm anguwar nan shiru kake ji ba motsin mutane sai kukan tsuntsaye na saman mangwaro. Badan fitulun sola da suka haske anguwar ba da duk jarumtar ka bazaka iya bi ka wuce ta cikin wannan layin ba. 




Shaguna duk a kulle sai shago daya wato na Muktar shi kadai ne a bude inda sabo an saba kowa ya watse a barshi shi kadai a gurin domin sai yayi lissafi tukun yake tashi. Zaune yake yana kirga cinikin da yayi yana washe baki domin yau anyi ciniki sosai a shago. Ta wutsiyar ido ya hangi kamar wani bakin abu na tafiya a kan hanya zai gifta ta kofar shagon shi. Da sauri ya dago kai dan ganin miye amma wayam.  




Komawa yayi yaci gaba da lissafin sa ba'afi seconds 30 ba ya kuma ganin wani jan abun kamar mutu kuma ya nufo shagon sa. Da sauri ya sake dago kai a karo na biyu nan ma baiga komai ba. Mamaki ne ya cika shi a fili yace "Kai miye haka kuma?". Ajiye kudin yayi ya fita waje a sauri ya wa-waiga ko ina har saman bishiyoyin wajan amma shiru baiga komai ba. Hakan tasa yace a zuciya "Ba komai kawai tsorata kaina ne nayi ashe". Juyowar da yayi da niyar ya koma shago yayi tozali da abunda yasa ya kwada ihu! Hade da faduwa dan razana. 



Ba komai idanunsa suka gani ba sai wannan yarinyar tsaye a kan kujerar da yake zaune. Fararen kaya ne a jikinta amma gaba daya sun baci da jini wuyanta a yanke jini na zuba har tsartuwa yake yi. Idanunta kuwa sunyi jawur jini na bulbula daga ciki haka hakuranta sun kara zarowa sun fito waje jini cike da bakin. Kuma a hakan murmushi take wani irin sauti na fita kadan-kadan.............



😰 Kodai aljana ya zane 🙆🏻??



Muje zuwa 


Karkuyi zatan labarin Aljanar fatima ya canza ne 😀fa








Autan writers KING BOY ISAH ✍🏻


👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 



Part 3-4



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽



Happy birthday

   ​UⓂⓂEIY ZEE​

         I'm happy for you 1+14 year. Lolz 


Hmm gaba dayan shi pagen naku ne yanda naga kuna nuna kauna a kan littafin tun kafin in fara har dauka nayi abun yayi yawa ashe abun yafi haka. Bansan ya zan misalta yanda kuke san littafin autan nan naku ba. Amma dai ga kyautar pagen a gare ku. Duk da nasan ban isa in biya ku da shi ba. 

 ​UⓂⓂEIY ZEE​

         PHATEEMA

         SHAZEE

            AUNTY ASY KHALIL 

           HAWWER. 


ALLAH YA BAR MUN KU YASA KUFI HAKA. ALLAH YA KARA MUKU BAIWA DA BASIRA. 



FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

Us whatsapp's number.

08096831009

----





Muktar da gaba daya ya tsorace ya gigice har ya fadi. A hankali y dago kai dan kara tabbatar da abunda ya gani shin ko gaskiya ne ko kuwa idanunsa ne kawai suka nuna mishi hakan. Abun mamaki a dagowar da yayi wayam yaga gurin ba komai. Yana nan dai a tsaye yana tunane-tunane wannan al'amari domin yasha kai karfe sha biyu amma tun da yake yau kusan shekara daya da bude shagon amma ba'a taba tsorata shi ba sai yau "shin ko dai da gaske gamo nayi" ya tambaya kansa.  




Karar da ta doki dodan kunnan sa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake. Daga bangaren hannunsa na dama karar Kofatu kamar duban dawaki ne suka nufo shi yaji. Nan da nan ya juya a firgice yana neman fadawa shago. Wasu bakaken hallitu ne wanda masu jikin doki dukan su bakake ne amma ba kai a jikinsu sune suka nufo shi a sukwane. 





Koda idanunsa sukayi tozali da wannan mugun abu, hankalinsa ne ya dugunzuma dan tsabar tsorata a million ya fada shago bai ko tsaya kulle shagon ba haka kuma baisan lokacin da ya tsallake dogon bincin da ke raba masu sayayya da cikin shagon ba. A bayan bencin ya sama wani dan lungu ya labe yana maida nunfashi day-day. Duk jikinsa karkarwa yake idanunsa nan-da-nan suka saki ruwa. Kuka ya farayi shabe-shabe ya fara magana a hankali cikin muryar sa dake rawa yana fadin "Wannan wane irin bala'i ne ni kam yau na shiga uku..." Surutai ya tayi shi kadai sai da ya dau kusan mintuna 20 a cikin shago yayi lumi ko motsin kirki baya yi kuma karar dawakin nan har yanzu a kwaita. 




Can dai yaga wannan bata yi ga zafin dake adabarsa sai gumi yake, hakan tasa shi fitowa daga inda ya labe a hankali ya dan leka kofar shagonsa wayan baiga komai ba sai karar da yake ji. Ya dade nan a tsaye ko zaiji karar ya ragu amma ba alamar raguwar. Ga zafin ya fara cin karfinsa ya fara magana cikin murya irin ta mai kuka ko gunguni. "Haba wllh fita zanyi bazan tsaya zafi ya kashe ni a banza ba. Wallahi fati zanyi ko me zai faru ya faru. Juyawa yayi ya dauki makulan shagon bai ko tsaya debe kudinsa ba. Ya fara yunkurin tsallakowa bayan ya tsallako ne ya bi a hankali kamar munahiki ya leko shagon ta bangaren da yake jin karar.  



Leka warsa keda wuya sai yaji kamar an dauke wuta dif! Karar ta dauke. Hakan ya bashi dama da karfin gwiwa na fitowa da sauri ya garkame kofar shagon yanufi hanyar gida da gudu-gudu sauri-sauri takun da yayi bai wuce 15 ba sai gani yayi wutacen nan gaba daya sun dauke dif!. Al'amarin da tasa shi yayi tsaye cik kenan. Kamar walkiya haka yaga wani farin abu ya gifta ta gaban shi duk da duhun amma yaga abun kamar mutun lokacin tsoro ya kara rufe shi, Suman tsaye yayi a gurin tsabar tsorata da yayi.  




Sanda aka shafe kusan mintuna 10 yana wajen a tsaye ya rufe idanu alamun haske ya gani hakan yasa ya bude idanunsa ai kuwa sai yaga wutar ta dawo. Nan fa ya ranci ta kare ya zura a guje kamar wanda zai tashi sama. Yana wuce wani mangwaro yajiyo dariya a saman shi, a cikin gudun ya wai-wayo abunda ya gani ne yasa shi har saida yayi tuntube karfin gudun yasa har sai da ya wuntsila yayi kungun bala. Yarinyar nan ya gani kamar dazun duj jini na fita a jikinta kuma itace ta dage kai sama tana gagaba dariya marar dadin ji.




Bai kula da ko yaji ciwo ko baiji ba. Ya tashi ya ruga a guje yana ihu. Bai daina ganin yarinyar na fito mishi a sifofi na ban tsoro ba har ya kawo gida. Da shigar sa gida ko tsayawa sa kubobin kawai banka kofar yayi. Dake yasan kyauran mai jamlock ne. 




Da gudu ya fada daki UⓂⓂEIY ZEEY

 (matarsa) na kwance a kan gado tana barci. Yabi ta kanta ya tsallaka dayan gefan tuni ya ja (blanket) bargo ya rufa duk zafin da ake fama da shi. Nauyin sa ne ya tayar da Ummiey daga barci waigawa tayi dan ganin waye sai ganin shi tayi ya kudun-dune cikin bargo yana sauke nunfashi day-day tayi mamaki mutumin da baya san zafi ko kadan kullum in yazo sai ya mayar da fanka ta bangaransa amma yau gashi ya shiga bargo lalai ba lafiya ba. 



"Mai gida-Mai gida baban HAWWER-baban HAWWER lafiya kuwa?" Haka ta dinga jero mishi tagwayen sunaye hade da dadabarsa tana tambayarsa. Karkarwa taga duk jikinsa ya hau yi. Domin shi kam abunda yake ji yayin da yake ji bashi take fada ba kuma ba muryarta yake ji ba. Domin wata murya yake ji mai abun tsoro tana fadin "Mu...ktar...m..u..ktra" a slow muryar ke tafiya.  



Ummiey ganin karkarwar da yake tayi yawa ta dan daga murya "Baban Hawwer lafiya kuwa". Yayin da shi kuma yaji an daga mishi tsawa da wata muryar mai razanarwa ance, "Kai muktar magana fa nake maka". Firgigit ya tashi zaune. Maimakon yaga matarshi ummiey. Yariyar nan ya gani kamar yanda take dazun dan yanzu ma tafi ban tsoro domin dogon gashin kanta mai-makon ya zuba a bayanta sai mikewa yayi tsaye cir! Yayi wani irin fadi A sama. ('Kai duk wanda yayi arba da wannan yarinya ala dole hantar cikinsa ta kada dan tsoro, In ma bai sume ba')




Muktar kuka ya farayi yana ja da baya-baya yana bata hakuri a haka har ya surmuyo kasa daga kan gado bai ko jira kuma ba yaci gaba da ja bayan. Ummiey na gannin mai gidan nata ya fado daga kan gado yana kuma kallonta yana kuka ta tabbatar da ba'a hayyacinsa yake ba. Hakan yasa ta matso daga kan gadon ta sakko a hankali take binshi tana tambaya. "Baban hawwer wai me ke damunka ne?, ka min magana mana".  



Yayin da shi kuwa yarinyar yake gani tana tunkaro shi hakan yasa ya kara sauri wajen jan gindin da yake yana yin baya yana fadin. "Na shiga uku yau naga ta kaina, dan allah kiyi hakuri karki kashe ni shin dan naki taimaka miki shikenan nayi laifin da za'a azftar dani har haka. *DAGA TAIMAKO* dan allah karki kashe ni". 




Ummiey da jin wannan kalamai na fita a bakin mijin nata sai tayi tsaye cik! Tana kallon shi cike da mamaki tana cewa "Lalai baban hawwer yau ba lafiya kake ba. Yanzu ni din kake cewa zan kashe ka ni?". 

Yayin da shi kuma yake jin wani abun daban sabanin abunda take fada. Domin shi yarinyar yaga ta tsaya tana gagaba dariya kafin ta fada da murya mai fitowa bibiyu. "Kai muktar ka sani ka debo ruwan dafa kanka, a cikin kifayen da kake kamowa yau ka kamo ajali ka. Nan take yaga wata wulshe-shiyar wuka ta bayyana a hannun yarinyar. 





Ihu! Ya fara kurmawa yana fadin "Wallahi na tuba baran kara ba, dan allah ki yafe min duk abunda kike so zan baki. Duk lokacin da kikaji yunwa ki dinga zuwa ina baki abinci ko da kuwa zakiyi ci Goma ne a rana amma dan allah ki taimaka kiyi min rai karki kashe ni". Ummiey taga abun da mijin nata yake ya fara yawa harda ihu nan ta fara tunanin ko ta leka ta kirawo makwabcin su ne. Kuma sai dai tace bari ta karasa gare shi. Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi................





Mujee zuwa.



Autan writers nee king boy







👺👽👽👽👽👽👽👺 


   *^^^^^^^______^^^^^*

    *ALJANAR FATIMA*

   *^^^^^^_______^^^^^*


👺👽👽👽👽👽👽👺 


Page 5-6



NA. 👑 KING BOY ISAH 👑




👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽


THIS PAGE DEDICATED TO YOU.


NASMAT 


ASMART


MARYAM AMIN


SIS HAFSAT


MMN AFNANN


KHADIJA BABY


KHADIJA 🤔


KHAIRAT 💃🏻


MMN SADIQ 


KAMALA MINNAH 


Love is my everything. It’s everywhere. It’s in the messages you send me, it’s in the words you say to me and it’s in your eyes when you look at me. Love is in my heart and in my thoughts. Love is you and me. 👆🏽 I love them ☺



FOLLOWING US AS:

----

Like us page.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

----

Check us blogger.

Zamaniwriters.blogspot.com

----

 Email us your comment and reports.

Zamaniwritersassociation@gmail.com

----

whatsapp's number 

08096831009

----






         *Karshen pagen baya...*

Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi» Ummiey gaba daya ta firgice kamar ta kurma ihu! Itama. Ganin mai gidan nan nata a kass sumame. A rude tayi waje tana zubda hawaye. Da sauri taje ta bude randar kasar ta wacce ruwan ciki yayi sanyi sosai kamar ansa kankara tasa moda ta kwalfo tayi cikin daki da gudu. 



Tana zuwa batayi Wata-Wata ba ta kwaraya mishi gaba dayan ruwan da ta debo. Firgi-git ya mike zaune yana nishi yana yan waige-waige kamar wanda yake neman wani abu dayan hannun sa kuma goge fuskarsa yake domin ruwanda Ummiey ta kwaraya mishi. Ganin baiga abun da yake zatan gani ba yayi saurin mikewa ya nufi kofar daki a guje ya rufe ya sakala kubobi biyu yana fadin. 



"Ummiey wllh kashe ni zatayi taimaka ki kama a jawo wardrobe din nan a kara rufe dakin". Ummiey kam tsaye tayi ta saki baki tana kallansa yanda duk yabi ya rikice yake abu kamar mahaukaci. "Baban hawwer wai lafiyar ka kalau kuwa? Ya kake wasu irin abubuwa ne haka wanda ban taba ganin kayi kwatan-kwacin kalar su ba?".  



Tsawa ya daka mata kamar yanda ya saba dama baya jiya mata dadi, ba dan Ummiey mai hakuri ce ba da tuni ta bar masa gidansa to amma sai akaci sa'a irin matan nan ne masu hakuri tayo gadon gidansu dake babban ta shine limamin masalacin juma'ar anguwar kuma baban malammi ne masani. Itama kuma haka tayi sauka har biyu. 

Zabura tayi tsawar da ya daka mata. "Nace miki kizo ki kama wannan wardrobe din mu kai mu rufe kofar aljana ce in ta sake shigowa kashe ni zatayi". 



Ummiey sai yanzu ta gane mijin nata gamo yayi. "Baban hawwer wacce aljana kuma"?. "Oh! My god ya fada. Tunda bazaki kama min ba baza ki taimakawa mijinki ba so kike ta halaka ni to bari in kai ni ai zan iya". Kiki-kiki ya jawo wardrobe har kofar dakin ya danne kofar. Danne wa keda wuya yaji an fara girgiza kofar dakin da gudu ya haye gado ya lulube. Ummiey ce tazo kanshi ta fara tofa mishi addu'o'i har allah ya taimaka barci yayi gaba da shi.  



Tunda asuba da ya tashi yaci gaba da zabur-zaburansa. Ummie na tofa mishi addu'a amma taga abun yafi karfita hakan yasa ta dauki waya ta kira babanta tana kuka ta gaya mishi duk abunda ya faru. Yace gashi nan zuwa. Mukhtar ba abunda yake sai surutai duk bayan yan mintuna kuma sai ya dinga tsorata yana boyewa yana fadar "gata nan gata nan".! Ummiey ita kanta ta shiga rudani. 



Ba'afi mintuna 20 ba malam hamza ya karaso gidan koda Mukhtar ya jiyo sallamarsa da gudu ya fito ya makal-kale malam yana surutai saida malam yayi da gaske tukun ya raba jiknsa da na Mukhtar lokacin ya fara tofa mishi adduo'i tukun ya samu haukan da yake ya dan lafa malam yasa shi ya zauna a tabarma da ummie ta shimfida. Bayan sun zauna ne malam ya fara karanta ayyatul kursiyyu tare da sauran ayoyi masu karfi. Ba'a dade da fara karatun ba sai ganin wannan yarinyar ta bayyana cikin kayan da Khadija ta saka mata. A gaban malam ta zauna hade da musu sallama. Muktar har zai ruga malam ya zaunar da shi. Hatta ummie ta tsorata domin ganin abun tayi kamar a mafarki. 



Malam ya kalle ta yace "baiwar allah me wannan mutumin ya miki an bani labarin irin azabtar da shi da kika yi jiya". Muryar ta ba dadin ji tace, "ka tambaye shi malam shi ai yasan abunda yayi". Malam baiyi gardama ba ya juya ga muktar ya tambaye shi me ya mata. "A tsorace yac malam wallahi ba abunda nayi mata shagona taje tana nuna alamun yunwa take ji a rana ta farko na kore ta a rana ta biyu kuma ganin ta takura min na dake ta". 



"Karya kake muna fiki azzalumi macuci, Ko daya ba dan wannan ne na shiga rayuwarka ba. Wannan ma nayi ne dan in tabbatar da rashin mutuncin ka da mutane ke fada sai naji kai da bakin ka ma fada kake. Malam muktar Shin har ka manta abunda kayi shekara daya da rabi baya da suka wuce?. Yarinyar ta fada cikin tsiwa tana hararen shi. Nan fa kwakwalwarshi ta shiga juya mai yana kokarin tuno wani abu. Ganin ya shiga dogon tunani ta sake daga mishi wani tsawan wanda ita kanta ummie ta firgita kamar ta fada daki taji. "Kaaaai! Mugu wato har ka manta yaron da ka kashe ka rabasu da dukiyarsu ka raba yaya da kanwa. a fadama ko?". Dummm! Gaban muktar ya fadi jin ta tado zancen da a tunaninsa ba wanda ya san shi daga allah sai shi sai kuma wannan yarinyar. (What!) "Yaron da ya kashe?". Ummiey da malam ne suka fadi hakan a tare. 




Bugun kirjinsa ne ya tsananta nan take jikinsa ya fara bari. Motsowa ya farayi gaban Yarinyar yana fadar "Dama ke aljana ce ban sani ba. Don allah ki rufa min asiri karki tona wannan sirrin duk abunda kike so zanyi amma ki taimake ni karki tona wannan sirrin...." Tsawar da ta daka mishi ce ta tsayar da shi nan take ta wani bata rai fuska ba wal-wala. "Bani bace domin dani ce da bazaka kwana ba a ranar. Ka basu labarin abunda ka aikata wa wannan yarinyar da kanka, in kuwa ba haka ba yanzu ka gayawa yan garin ku". Ta karashe maganar cikin daga murya. Nan take tsoran Mukhtar ya karu. "To-to bari in fada amma dan allah karki min komai".  



Malam da diyarsa ba abunda suke sai kallo da sauraren ikon allah. Ummiey tunani take shin wannan wane BOYAYYEN AL'AMARI ne? Wanda bata sani ba game da mijinta. Ita dai bayan mugun halin sa da kowa yasan da shi bata kuma san da wani ba. Mukhtar ganin kowa yayi shiru shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani mugun kallo mai tsoratarwa. Ya shiga basu labari..............................




Mujee zuwa.



Autan writers nee king boy


Comments