SON GASKIYA BOOK 2 Hausa novels

πŸ’žπŸ’ž SAN GASKIYA πŸ’žπŸ’ž

BOOK 2

part 63 - 64
NA.  πŸ‘‘KING BOY ISAHπŸ‘‘
............................................................
. ................................
...........
this page dedicated to u  *Kamal Muh'd dambu*...
.............
.....................................
............................................................

__________________________
🌟 ZAMANI WRITERS MAY 2017 🌟
|_________________________|


***** zamani  *****
🌟ZAMANI WRITER'S ASSISTION 🌟  © Z.W.A
***** zamani *****


DUKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH S.W.T tsira da aminci su dad tabbata ga shigaban mu masoyin mu mai kaunarmu annabi MUHAMMADU S.A.W

MUNA ROKON ALLAH YASA CETAN SA YA RISKEMU ALLAH YASA YA CECE MU RANAR DA  ZA'A RASA  MAI CETO SAI SHI. ameen

........ ci gaban littafin Son gaskiya kenan. A karshen littafi na daya mun tsaya a Wannan.....

amma fa wllh maman amir sai nayi wa abdul din nan wulakan ci domin ya gane kuskuran da ya tafka kinga gobe bazai kara ba.

haba nadeeya abdul fa mutumin kirki ne inaga sabani dai aka samu tsakaninku


ko kuwa mantawa yayi. hmm to mmn amir bari inje in dan yi wanka domin na gaji to jeki bari insa mairo ta kawo miki jakar ki daki. ****
sanye take da hijab dogo wanda ya kawo mata har gwaiwa kayan atamfa ce mai tsada riga da siket duk inda ta nufa ko ta gifta ba abunda zai biyo baya sai kamshin wani mayen turare tafiya take yi tamkar bata san taka kasa.


fahad  da suke zaune su uku a library shine ya fara jin kamshin turaren hakan yasa shi juyawa. shiru yayi ya zurawa wajen ido bai karashe maganar da yake yi ba. saleena ce ya ga ta nufo su cikin shiga ta alfarma.

tasa hijab shi kam bai taba sanin haka yarinyar nan take da kyau ba sai yau nan ya tabbatar da cewa gaskiya hijab ba karamin fito da kyawan mace yake ba abokan sa ma ita suka tsare da kallo.*****


husnah kuwa ta wani rame duk jijiyoyin wuyanta sun fito kullum mafarkin abdul take hk kullum cikin zarya take zuwa gareji neman abdul amma oga yace shi baima san wanene abdul ba wai shi tunanin sa abdul wani laifin ya aikata domin yarinyar kullum sai taje. 


mum tayi tayi amma husnah taki gaya mata cutar da ke damunta idan ta tambaya sai dai husnah tace ba komai.

yau zasu koma abuja tayi tayi a barta a nan ko data kara ganin abdul dinta amma mum dinta taki mum dinta tace tunda kinki ki fada mana abunda ke damunki  idan muka koma can sai a auna ki a fada mn.

bazan iya barinki a nan cuta ta kashe min ke ba gashi anrasa me ke damunki.

husnah ba yanda ta iya dole ta hakuri suka tafi abujan.
*******

a hankali saleena take tafiyan har ta karaso gare su tayi salama. cikin wata sasayar murya mai dadin saurare.  ita kanta tayi mamakin ganin fahad ne ya fara amsa sallamar saidai ya kauda kansa daga kallanta.har kasa ta durkusa kamar mutuniyar kirki ta gaishe su "ina kwananku". dukan su cike da mamaki suka amsa "lfy lau". ya gida ta maida musu da cewa gida lfy lau saidai duk maganar da akeyi ta zuba ido ne ga jarumin nata wato fahad shi kuwa ya wani sha kunu gefe ma yake kallo tunda ya amsa sallamar to baice ufan ba.


bayan sun gaisa tace anan ake hutawa. karkaso kaga wangale baki gun abokansa yau gasu suna hira da saleena yarinyar da ko a titi kuka hadu baka goce mata ba sai tasa guard dinta sunyi maka dan banzan duka sun barka nan kwance.


gaba daya kamar hadin baki suka ce eh wllh muna nan muna hutawa kafin a shiga aji. tace wannan yayi kyau ai. hira suka sha sosai dake abokan fahad din akwai masu surutu ku can da balle yanzu an sama mace macen ma budurwa maiji da kanta ai hira sai in ba'ayi itama kuma haka ta ware kamar can dama mai surutu ce ita kuwa tana yi ne dan sahibin nata yasaka baki ko ta sama shiga.


amma kamar kurma haka ya koma musu ko kallanta bayayi sai ta hutsiyar ido  yana lure da ita tana satar kallan sa. can dai da taga baya da niyar magana tace wai shi abokin naku baya magana ne.?
wane fahad din tabb magana kai ai wannan in ya tashi yanda kika san gidan redio haka yake. murmushi ta danyi mai hade da yar dariya kadan tace to ai ni nagan shi shiru ne ko dai nice baya san gani shi yasa naga duk ya bata rai.  "ai kinsan yanayin nasa ne haka kamar mai aljanu yake so kinga in abun ya juyo dole kiga hakan na faruwa." Da sauri fahad ya juya yawa wanda yayi magana kulli a baya yace, "dan rainin (sense) Hankali, nine ma mai aljanu ko to bari kaga aljannu kuwa..........................................

king boy

little of writer
πŸ’ž SON GASKIYA πŸ’žπŸ’ž

BOOK 2

part 65 - 66NA.  πŸ‘‘KING BOY ISAHπŸ‘‘
............................................................
. ................................
...........
this page dedicated to u Aunty maryam yaqub...
.............
.....................................
............................................................

__________________________
🌟 ZAMANI WRITERS AUG 2017 🌟
|_________________________|


***** zamani  *****
🌟ZAMANI WRITER'S ASSISTION 🌟  © Z.W.A
***** zamani *****
Cike da murmushi saleena tace,  "a'ah yayah fahad ayi mishi hakuri kar a nuna mishi aljanu domin ko ni nan baxan so ganinsu ba".

  kallonta yayi a fuska ya danyi wani murmushi wanda zamu iya kira yak'e. a zuciya kuwa yaji dadin maganar ta sosai bama kamar ce mishi yaya da tayi shida a duniya yana so yaji an kira shi da yayah. 

Tun daga ranar saleena bata da wajen zuwa sai gunso a nan take hira. da kadan kadan dai har fahad ya fara sakar mata fuska.

kamar kullum yauma taje ta zauna sai taga fahad na da-daure fuska, "Abokaina bari in baku wani labari mai ban tausa" gabada suka juyo kanta yauwa muna jinki. shi kuwa Fahad kansa a kan wani littafi dake hannunsa yana jinsu amma ko kallon gefan da take bayayi,

  "Akwai wani zomo kyakyawa a ciki wani daji dake nesa da mutane, shi ya kasance dan jiji da kai ne ko mai nasa na daban ne, Wata rana wata Zomowa ta kawo musu Ziyara a lokacin data dora idanu a kan wannan zoman  sai taji duk duniya ba wanda take so sai shi.

sbd haka ta zauna a dajin saboda shi a kullum sai tazo gidan su zomo daga ta ganshi shikenan sai ta koma, A kwana a tashi har sauran zomaye abokansa dama shi kansa suka fahimci zomuwa sanshi take.

shi kuwa a lokacin ya nunu baya santa ko kadan suka tambaye shi don me?. yace kawai bata da kunya ne kuma bata girmama na gabanta dama wasu halayen nata marar kyau, zomaye suka ce to idan ta gyara zaka sota?

. yace sosai ma, ashe zomuwa tana labe tana jinsa, hakan yasa ta gyara halayen ta marar kyau tazama wata salaha, .duk da gyara halayya da zomuwa tayi.

zoman nan bai sota ba kuma kollom sai ta zo gidansu, tsabar so ma idan ta sama karas bata fara ci sai ta kawo kofar ramin Zomo sannan sai ta Raba biyu taci Rabi ta bar mishi Rabin,
In takaice muku labarin dai karshe zomuwaπŸ‡ Rataye kanta tayi a bishiya.

sai zuwa akayi aka same ta a mace πŸ‡
bayan anyi bincike aka gano cewa sanadin San zomo ne ta Rataye kanta, abokansa sukaje suka sanar da shi cewa Zomuwa ta Ratayi kanta πŸ‡πŸ€” Zomo yayi bakin ciki sosai sai yaji dama ya yarda ya karbi soyayyarta, kurunkus πŸ”š 

Saleenah tace labari ya kare, Ga  tambaya a gare ku shin a mutane hakan yΓ  taba faruwa?

Wani daga cikin samarin gurin yace, sosai ma hakan tasha Faruwa, idris yace haba wace mahaukaciya ce zata yarda ta kashe kanta dan saurayi yaki santa a wannan zamanin ai bazai taba yuyuwa ba.

lokacin Saleena ta mike tace ai kuwa yau hakan zata fara faruwa idan bata taba faruwa ba idan kuma ta taba faruwa za'a maimaita, tana gama fadin haka ta wuce da sauri tana goge kwallah data cika mata ido.

motar ta taje ta hau yanayin jan datawa motar kadai ya isa ya shaidama wannan ba lafiyanta lau ba ko kuwa kace Sauri take zata mika wani wanda ke Rai hannun allah asbiti.

Su idris kallon-kallo suka shiga yi, wani yace kai wannan yarinyar fa wllh da gaske take kanta zata kashe, Idris yace ai naga alama nima tun da ta fara Labarin na lura na gane cewa da Fahad take.

Fahad dan allah tashi muje mu ceci Rayuwarta pls fahad. Fahad din ko kallonsa baiba, Idiris ya mike Fahad (pls u only can save her life pls) A kan sanka fa ta chanza tabar munanar shiga ta zama Salaha ta Rabu da duk kawayenta mu abokanka mu muka zama  kawayenta.

Fahad *SON GASKIYA* saleena ke maka wanda nasan a yanzu Abun ne ya isheta sanka ya fara neman illatata sakamakon Rashin amincewarka shi yasa take neman kashe kanta dan haka kayi hakuri koma bazaka amince ba ka taso muje mu ceci Rayuwarta lokaci na Kure wa fa!.

  Fahad ya warce hannunsa daga Rikon da Idiris din ya mishi yace, To ni ina ruwana bari kaji to ba inda zanje idan bata da hankali ai sai taje ta kashe kanta din"  Idiris da yaga lokaci na kurewa da gudu yaje ya hau mashin dinsa a million ya fita shima,

yayi gudu Sosai tukun ya hangi motar Saleena sai hauka take da mota a kan titin  idan yaga tayi wani abun har dafe kai yake domin ganganci ne take,

Can yaga ta saki titi tabi wani jan birji da ya nufi jeji,  gudu take sosai domin duk inda ta wuce Kora sai ta bide bayanta, hakan yasa ya kasa cin mata,   har tayi mishi nisa kwarai.

Saleena bata zame a ko'ina ba sai gindi wata tsohuwar rijiya mai zurfi. Tana fitowa kuwa ta cire hijab din dake sanye a jikinta sannan ta cire takalmin ta fuskarta ba abunda zaka gani in banda hawaye dake rigee-rigen   zuba kasa, Bakin rijiyar taje ta hau tukun ta bude baki ta fara magana cikin kuka.

Ban rasa ci ba ban rasa sha ba, Ina cin duk abunda nake so ina kuma shan duk abunda nake so, inayin duk abunda naga dama. Kudi ko nawa ne basa gagarata. Amma duk da haka na rasa farin ciki na. Lalai So muguwar cuta ne bama kamar in ka so wanda baya sanka. Ban taba shiga kunci da damuwa ba sai da na shiga duniyar masoya.


Lokacin ta saki wani dan guntsun murmushi hade da cewa. "Fahad kenan sai da na kamu da soyayyar ka, tukun nasan ko miye so. Bani da tunani sai naka bani da zance sai naka. Na canza gaba daya na lalace nayi iya iyawata domin ka aminta dani ka karbi soyayyata amma kaki.

Ka guje ni a lokacin da sanka yayi min illah. Kamar yanda wasu masoyan ke cewa masoyansu (Ka zamto rabin jikina, jinin jika na.) Su suna fada ne domin kawai masoyan nasu suji dadi. Amma ni kuwa da gaske ka zama jinin jikina Rabin raina. To in kuwa haka ne rayuwata bata da wani amfani in babu kai. Dan haka bissalam Fahad sai wani jikon. Da gama fadar haka ta yunkura da niyar fadawa cikin ba zato ba tsammani sai ji tayi an riko hannunta da sauri ta juyo dan ganin waye. Tana juyo wa kuwa ya dauke ta da mar, ji kake Tass!.........

*Zanci gaba*

*Autan writers  King boy*

Comments