Sharri Kare Ne Part 7 Littafin Dare Dubu Da Daya

 SHARRI KARE NE 7



HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI


Waziri Aku 


Mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa don yin wanka. Yaran nan suka himmatu wajen hidimta musu. Duk wanda ya yi wanka sai su taje masa kansa kamar yadda Abusir ya koya musu. Mutane suka yi ta zuwa suna yin wanka, tsawon kwana uku ba a karɓi dirhami ko ɗaya daga hannun kowa ba.


A rana ta huɗu Wanzami ya gayyaci Sarki zuwa ga gidan wanka. Sarki ya yi hawa da tawagarsa duka, suka nufi gidan wanka. Abusir ya tarye su kyakkyawar tariya. Ya kai Sarki wani ɗaki na musamman domin yin wanka. 


Sarki ya tuɓe tufafinsa ya shiga cikin kwatarniyar wanka, Abusir ya samu soso da sabulu mai ƙamshi ya riƙa cuɗa bayan Sarki yana fitar masa da dauɗa kaɓaki-kaɓaki. Duk sadda ya kankaro dauɗa sai ya nuna wa Sarki, shi kuwa ya yi ta mamaki. 


Wanzami bai gushe ba yana cuɗa Sarki har sai da ya ji fatarsa ta yi santsi kamar ta kifi, dauɗar jikinsa duka ta fita, sa'annan ya samu ruwan wardi ya ɗauraye masa jikinsa, ya tsane masa ruwa da mayafi mai laushi, ya yayyafa masa turare. Ya sa yaran nan suka taje masa gashin kansa. Sarki fa ya ji jikinsa ya yi garas kamar ba nasa ba, sai wani sabon ƙarfi yake ji kamar aholakin jaki. Ya ji ta ko'ina sai iska mai daɗi ke shigar sa. Ya dubi Wanzami ya ce, "ashe haka gidan wanka yake?"


Abusir ya ce, "I, Allah ya taimake ka."


Sarki ya ce, "Wallahi birni kuwa ba ya cika birni muddin babu irin wannan a cikinsa." Ya yi ta mamaki yana tu'ajjibin wannan abu, ashe su zaune kurum suke ba su san daɗin duniya ba. Ya yi wa Allah godiya da ya kawo musu Wanzami wannan gari domin su ɗanɗani daɗin gidan wanka. 


Ashe dai tuntuni kallon ƙauyawa baƙin da ke zuwa garin ke yi musu, sai yanzu da wannan baƙo ya zo ya fid da su kunya. Daga nan Sarki ya ce wa Wanzami, "to nawa za ka riƙa karɓa ga duk wanda ya yi wanka?"


Abusir ya ce, "duk abin da ka yanke, shi za a karɓa, ranka ya daɗe."


Saboda santin wanka da Sarki yake yi da kuma daɗin da ya ji, sai ya ce, "in haka ne kuwa duk wanda ya yi wanka ya kamata ya biya dinari dubu, ko ma sun yi kaɗan ne a ƙara."


Abusir ya yi murmushi ya ce, "Allah ya taimake ka, kuɗin sun yi yawa. Ba duka mutane suka zama ɗaya ba, akwai mawadata da talakawa a cikinsu. Idan aka ce kowa ya biya dinari dubu, talakawa ba za su iya biya ba, mawadatan ma ba za su juri biyan wannan kuɗi ba kullum, yau da gobe sai Allah, watarana sai a wayi gari babu mai zuwa wanka a gidan."


Sarki ya ce, "to, nawa kake gani za ka iya karɓa?"


Abusir ya ce, "abin da na ga ya fi shi ne kowa ya biya gwargwadon ƙarfinsa. Mawadata su biya gwargwadon nauyin lalitarsu, su ma talakawa su biya ɗan abin da suke iya biya. Ta haka sai kowa ya amfana da gidan wankan. Amma biyan dinari dubu wannan sai Sarki kaɗai ke iyawa."


Babban Alƙali da ke wurin ya tsolma baki ya goyi bayan Abusir, ya kuma ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara ai wannan karimci na biyan dinari dubu ba wanda ke iya shi sai fa kamar kai Sarkin adalci."


Sarki ya ce wa Alƙali, "ka yi gaskiya. Amma wannan mutum baƙo ne da ya kawo mana abin alherin da ba mu taɓa zato ba a garinmu, ya fid da mu kunyar baƙi da ke zuwa kasuwanci, ai kuwa ya kamata mu nuna masa mun ji daɗin wannan alheri, mu karrama shi iyakar ƙarfinmu, an ce yaba kyuata tukuici."


Fadawa suka karɓa, "gaskiya ne Sarkin duniya. Amma kuma, Allah ya ba ka nasara, ba ƙaramin aikinka ba ne idan ka ɗauke wa talakawanka biyan kuɗin wanka a nan, duk abin da za su biya, kana iya biyan shi cikin arzikinka, albarkacin kaza, kadangare ke shan ruwan kasko."


Sarki ya ce, "to, shi ke nan. Amma duk wanda muka zo tare yau, ya biya dinari ɗari kuɗin wanka, ya kuma ba wannan baƙo kyautar baƙin bawa ɗaya da farin bawa ɗaya da kuyanga ɗaya."


Muƙarraban Sarki suka amsa gaba ɗaya, "mun ji mun amince ya Sarki. Amma muna roƙon alfarma daga yau a bar mu mu riƙa biyan abin da ya sawwaƙa idan mun yi wanka."


Sarki ya ce, "babu laifi ga wannan."


Mutanen nan suka kawo duka abin da Sarki ya ce, suka damƙa wa Abusir. To, tawagar nan da Sarki ya zo da ita, waɗanda suka yi wanka, mutum ɗari huɗu ne. Don haka suka tara masa dinari dubu arba'in da baƙaƙen bayi ɗari huɗu da fararen bayi ɗari huɗu da kuyangi ɗari huɗu. Sarki kuma ya kawo dinari dubu goma ya ba shi, ya ƙara masa da baƙaƙen bayi goma da fararensu goma da kuyangi goma.


Yayin da Abusir ya ga an tara masa wannan dukiya haka, sai ya tafi gaban Sarki ya durƙusa ya ɗauki ƙasa ya ce, "ya Sarkin adalci mai yawan kyauta, ina zan sa waɗan nan bayi haka?"


Sarki ya bushe da dariya, ya ce, "Allah Sarki, talaka dai talaka ne. To ina ƙudan yake balle romonsa? Yanzu waɗan nan 'yan bayin har gani kake sun yi maka yawa? Ka sani mun ba ka su ne ko da wata rana sha'awar garinku ta faɗo maka a rai, sai ka tafi da abinka can, ka zauna da iyalinka cikin wadata."


Abusir ya ce, "Allah ya ɗaukake ka, ni dai da kuɗi ka ba ni maimakon bayin nan da na so. Talaka da ni, ina na ga zarafin ciyar da wannan runduna balle saya musu tufafi, wannan ai sai Sarki."


Sarki ya yi kekkewa ya ce, "gaskiyar ka. To, ka sayar mini da kowane ɗaya dinari ɗari?"


Abusir ya ce, "na sayar maka, Allah ya ba ka nasara."


Sarki ya sa Ma'aji ya je taska, ya ƙidayo kuɗi ya kawo wa Wanzami. Abusir ya karɓa ya yi godiya ga Sarki ya kuma ce masa, "na gode da ka raba ni da wannan gayyar bayi da babu mai iya cishe su sai Sarki, Allah ya ba ka nasara."


Sarki ya bushe da dariya, ya kuma ce wa muƙarrabansa kowa ya ɗauki bayinsa da ya bayar, ya ba su kyauta. Suka shirya suka juya gida, suka bar Abusir yana ta faman ƙidaya kuɗi yana shirya su wuri guda yana ƙullewa cikin jakunkuna. Bai gushe kan haka ba har dare ya raba. Ya tara jakunkunan kuɗi masu yawa, ya kuma riƙe bayi ashirin baƙaƙe da wasu ashirin farare da kuma kuyangi huɗu da za su yi masa hidima.


Kashegari Abusir ya buɗe gidan wanka, ya tura mai shela cikin gari yana cewa, "kowa ya yi wanka yau a gidan wanka, ya ajiye abin da yake iya biya gwargwadon ƙarfinsa, kada wanda ya tsananta wa kansa." Shi kuwa ya samu kujera ya zauna a cikin zauren farko, ya ajiye ƙaton akwati kusa gare shi inda za a riƙa sanya kuɗi.


Mutane suka yi ta zuwa giye-giye suna yin wanka suna saka kuɗi cikin akwati, kafin rana ta faɗi akwati ya cika da kuɗi. Ana nan kuma sai Uwargidan Sarki ta aiko cewa gobe za ta zo ta yi wanka da tawagarta. Don haka sai Abusir ya sa aka sake yin shela cewa, gobe maza za su yi wanka daga safe zuwa tsakiyar rana, sauran yini kuwa na Sarauniya ne da mutanenta.


Washegari da yamma Sarauniya ta zo yin wanka, to da ma Abusir ya zaɓi kuyangi huɗu ya koya musu duk yadda za su cuɗa mutum su fitar masa da dauɗar jikinsa, kuyangin nan suka wanke Saurauniya fes suka feshe ta da turare. Ta ji daɗi, ƙirjinta ya yalwata don farin ciki. Ta ba Wanzami dinari dubu, muƙarrabanta ma suka yi masa ruwan kuɗi, suka tafi. 


Haka dai Abusir ya ci gaba da kula da gidan wanka, duk wanda ya zo, talaka ko tajiri, a kan girmama kowa ba tare da nuna fifiko ba. Sarki ya kasance ya kan zo gidan wankan nan duk sati, idan kuma ya zo ya kan saka dinari dubu a cikin akwati. Arziki ya yi ta kwararo masa kullum kamar ruwa. Ya yi abota da manyan fadawan Sarki. Labarin gidan wankan nan ya barbaɗu ko'ina cikin gari, kowa burinsa bai wuce a ce ya yi wanka a cikinsa ba. Wannan ke nan game da Abusir Wanzami.


Amma Abuƙir kuwa sai ya ji kullum ba labarin da mutane ke yi sai na wani sabon gidan wanka da aka gina a garin. Rannan ya ji wasu mutane biyu na hira, ɗaya na ce wa ɗaya, "kai wane, ashe haka gidan wankan nan yake? Wannan gidan wanka ai shi ne aljannar duniya. Wanda ko duk ya yarda ya mutu bai yi wanka cikinsa ba to ya yi wa duniya shiga shantun ƙadangare, a shiga da gudu a fita da gudu." 


Ɗaya mutumin ya ce, "ai insha Allahu gobe sai na je na yi wanka cikinsa, kada a kwashe daɗin duniya mutum na nan sake da baki."


Da Marini ya ji haka sai ya ce a ransa, "kai, ya kamata dai in tafi gidan wankan nan, in ga abin da mutane ke ta giɗaɗawa, an ce gani ya kori ji." Ya sanya tufafinsa masu kyau ya hau alfadara, ya tafi tare da bayi, huɗu na yi masa zagi, huɗu na dafe da kuturi har suka isa bakin ƙofar shiga gidan wankan. 


Ya ga mutane sai shiga da fita suke yi babu ƙaƙƙautawa, ga kuma ƙamshin turaren wuta ya game ko'ina gwanin daɗi. Ya sauka daga kan alfadara, ya kutsa kai cikin zauren farko, sai ya ga Abusir zaune a kan kujera. Yayin da Abusir ya ƙyalla ido ya gan shi, sai ya miƙe tsaye.


Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.


Me kuke tsammani zai faru a wannan haɗuwa ta biyu? Ko Abusir zai rama wulaƙancin da Marini ya yi masa?


Bukar Mada

22/10/2022

Comments