Sharri Kare Ne Part 5 Daga Littafin Dare Dubu Da Daya

 SHARRI KARE NE 5


HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI


Waziri Aku 


Sarki ya sa aka ba Abuƙir tufafi na alfarma. Aka je barga kuma aka zaɓo masa ingarman doki. Sarki kuma ya ƙidaya dinari dubu ya damƙa masa ya ce, "riƙe wannan ka riƙa ɓatarwa kafin a kammala gina maka marina." Aka ba shi ƙerarren gida cike da kayan alatu, aka haɗa masa da bayi biyu da za su yi masa hidima. 


Abuƙir ya kwana gidansa, da gari ya waye ya sanya tufafin nan na alfarma, ya hau doki yana taƙama, kamar shi ne Sarkin, mai ƙudundune a batta idan ya samu shantu sai ya miƙe. Magina suka shige gaba yana biye da su, suka yi ta zagaya birni har suka iso wani wuri a tsakiyar garin. Abuƙir ya dakatar da su ya ce, "nan ya yi mini yadda nake so."


Magina suka kwashi mai wurin sai gaban Sarki. Aka yi wa wurin kuɗi, Sarki ya biya fiye da yadda aka ce. Mai wuri ya karɓa yana ta godiya. Masu gini kuma suka duƙa aiki, lailatan wa naharan, ba ji ba gani. Abuƙir ya tsaya a kansu yana ba su umurni, "ku gina abu kaza nan, ku gina abu kaza can, ku sanya abu kaza nan, ku sanya abu kaza can." Cikin 'yan kwanaki kaɗan aka gina marina wadda babu tamka tata.


Da aka ƙare aiki, sai Abuƙir ya tafi gun Sarki ya faɗa masa. Sarki ya tambaye shi me ake bukata kuma? Abuƙir ya ce kayan aiki. Sarki ya lalubi lalitarsa, ya ƙidaya dinari dubu huɗu ya ba shi ya ce, "je ka maza ka sayi duka abin da kake bukata na aiki, ni dai na ɗokanta in ga yadda launukan nan suke."


Abuƙir ya ƙulle kuɗi ya nufi kasuwa tare da bayi. Ya tarar da baba tari guda, ga kuma araha, ya kwashi wanda zai ishe shi ya biya, ya kuma sayi duk wani abu da yake bukata na rini, bayi suka kinkima suka kai masa marina. Da ya ga komi ya kammala sai ya sake komawa wurin Sarki ya faɗa masa. Sarki ya yi murna ƙwarai sa'annan ya ce, "to, madalla. Sai a fara da ni, kasan kowa ya ci ladan kuturu dole ya yi masa aski." Ya tattaro tufafi kamar ɗari biyar ya ce a rina su launuka mabambanta. 


Abuƙir ya tafi marina ya duƙufa aiki, cikin ƙanƙanin lokaci ya rine tufafin Sarki duka, kowace tufa da irin launinta. Ya shanya su gaban shagonsa domin su bushe. 


Yayin da mutane masu wucewa ta gaban shagon suka ƙyalla ido suka ga tufafin nan, sai suka tsaya, suka yi cincirindo suna kallo, tare da mamakin launukan da ke jikinsu, waɗanda ba su taɓa gani ba tunda suke. Suka riƙa tambayar Abuƙir sunayen launukan, shi kuma yana faɗa musu, "wannan ja ne, wannan tsanwa ne, wancan kuma rawaya." Ya yi ta faɗa musu sunayensu. Nan da nan masu ido da kwalli daga cikin mutanen suka ruga gida suka kwaso tufafinsu suka kawo masa, suna rige-rige. Wani ya ce, "rina mini su rawaya." Wani kuma ya ce rina mini su makuba." Suka ce kuma ko nawa ya bukata gare su, za su ba shi.


Da ya gama aikin Sarki, sai ya ɗauka ya kai masa. Sarki ya karɓa ya riƙa dubawa yana al'ajabi. Ya yi farin ciki matuƙa, ya kawo kyautar dukiya mai yawa ya ba shi. Ko da fadawan Sarki suka ga haka, sai su ma suka ɗebo nasu tufafin suka ba shi. Sa'adda ya rina ya kawo musu, suka yi ta ba shi dinari da azurfa, suka girmama shi, darajarsa ta ɗaukaka ga Sarki da fadawa. 


Sunan Abuƙir fa ya yi tambari ko'ina cikin garin nan har mutane suka sanya wa marinarsa suna Marinar Sarki. Ko'ina sai kawo masa aiki ake yi, shi kuwa sai abin da ya yanka na kuɗi ake biyan shi. Sauran marinan garin kuwa tuni ya kashe musu kasuwa, ban da hamma ba su komai a ƙofar shagunansu. Duk da haka babu mai ikon ce masa kanzil a cikinsu, ana tsoron su inna inji ɗiyan mayya, to su ma tanka su ga aiki da cikawa gun Sarki. 


Saboda haka sai marinan nan suka sake dabara, tunda an ce in laila ta ƙiya sai a koma basha, suka riƙa lallaɓowa wurin Abuƙir suna ba shi haƙuri tare da yi masa daɗin baki wai ko sa samu ɗan abin kore wa bakinsu ƙuda, ba su san cewa rowa a gunsa ko na goye na shafa masa lafiya ba. Wanda hannunsa yake dunƙule kullum kamar hannun 'yan dambe. Da suka ga dai ba za su ɓamɓari komai ba ta hanyar bambaɗanci sai suka fara doddofar ya ɗauke su aiki, ya ɗan riƙa 'yammusu na cefane. Nan ma dai ya baɗa musu ƙasa a ido, ya kuma yi musu kora da hali, wadda aka ce ta fi kora da kara. 


Cikin 'yan watanni Abuƙir ya tara dukiya mai yawa, ya mallaki bayi da kuyangi, baƙaƙensu da farare. Duk inda ya ratsa cikin gari a kan dokinsa, sai talakawa ke faɗuwa suna kwasar gaisuwa suna faɗin, "maigida barka da fitowa." Bayi kuma na kewaye da shi suna yi masa hidima, da zarar ya ba da umurni sai su zabura su aikata. Wannan ke nan game da lamarin Abuƙir Marini.


Amma abin da ya kasance ga Abusir Wanzami, lokacin da Marini ya kwashe masa kuɗi ya kuma rufe shi cikin ɗaki a halin rashin lafiya mai tsanani ya gudu, ya kasance cikin ɗimuwa da gushewar hankali tsawon kwana uku bai farfaɗo ba. 


A kwana na ukun ne da yamma mai kula da gidan baƙin na zagayawa daga wannan ɗaki zuwa wancan har ya iso ga ɗakin da Wanzami yake ciki, ya tarar da ƙofa rufe, sai kuma ya tuna tsawon kwana uku bai ga duhun kowa daga cikin mutanen biyu ba. Ya ce a ransa, 'a'aha, waɗannan guduwa suka yi don kada su biya ni kuɗin haya. To, ban yardar musu ba." Ya sa ƙafa zai wuce, sai ya ji kamar nishi na fitowa daga cikin ɗakin. Ya tsaya ya saurara da kyau, ya ji lallai dai mutum ne ke nishi, ga kuma ƙofa a rufe. Ya tafi ya ɗauko wani ɗan mabuɗi na ɗakin ya buɗe, ya tarar da Wanzami kwance yana juye-juye yana kiran sunan Abuƙir.


Mai gidan baƙi ya yi maza ya durƙusa kusa ga Abusir yana cewa, "me ya same ka? Ina ɗan uwan naka?"


Cikin ƙarfin hali Abusir ya ce, "ba ni da lafiya, yanzu na farfaɗo. Na kirayi abokina ban ji ya amsa mini ba. Don Allah laluba ƙarƙashin shimfiɗar nan da nake kwance ka ɗauki kuɗi ka sayo mini abinci, yunwa nake ji."


Mai gidan baƙi ya laluba ko'ina bai samu kuɗi ba, ya ce, "babu komai a nan."


Abusir ya tambaye shi, "ko ka ga abokina?"


Mai gidan baƙi ya ce, "yau kwana uku ban gan shi ba. Kai, ni ina tsammani shi ya kwashe ma kuɗi ya gudu."


Ran Wanzami ya ɓaci, Me ya sa Abuƙir zai yi masa haka? Don me zai kwashe masa kuɗi ya gudu ya bar shi cikin ciwo? Amarya ba ta hau doki ba, kuma sai a ɗora mata kaya? Hawaye ya kwaranya bisa kundukukinsa kamar ruwa don baƙin ciki.


Yayin da Mai gidan baƙi ya ga halin da Wanzami ya shiga, sai tausayi ya kama shi ya ce masa, "kwantar da hankalinka. Shi kuwa abokinka, rabu da shi, duniya ce ta ishi kowa riga da wando, wanda bai zo ba ma tana jiran sa balle wanda ke cikinta. Kuma shi sharri kare ne, mai shi yake bi." 


Ya tafi ya dafa shayi, ya zuba madara da gahawa, ya kawo wa Abusir domin ya sha hanjinsa su warware. Ya kuma tafi ya sayo masa abinci mai rai da lafiya ya kawo masa. Mai gidan baƙi ya yi ta jinyar sa tsawon wata biyu. Wanzami ya murmure sarai, jikinsa ya fara komowa. Ya yi wa mai gidan baƙin nan godiya sannan ya ce, "ina roƙon Allah ya hore mini, in biya ka kuɗin duka ɗawainiyar da ka yi mini."


Mai gidan baƙi ya ce, "ban yi don ka biya ni ba. Na yi ne domin neman yardar Ubangiji."


Daga nan Abusir ya saɓa zabirarsa ya shiga gari yana zagayawa, kamar yadda ya saba yi a baya. Yana cikin tafiya har Allah ya kawo shi kusa da marinar Abuƙir. Ya hangi mutane sun yi dafifi a gaban marinar suna kallon tufafin da aka shanya. Abusir ya tari wani mutum ya tambaye shi, "bawan Allah, ko lafiya na ga mutane sun taru gaban wancan shago?"


Mutumin ya ce, "hala kai baƙo ne da ba ka san Marinar Sarki ba?"


Abusir ya ce, 'Marinar Sarki?"


Mutumin ya ce, "I, marina ce da Sarki ya gina wa wani baƙo da ake ce ma Abuƙir gwanin rini. Duk sadda ya fid da launin da ba mu taɓa gani ba sai mu taru muna kallo muna tambayarsa sunan launin. Sa'adda ya zo garin nan sai da ya bi dukkan marinan garin nan yana roƙon su ɗauke shi aiki, amma suka kore shi." 


Mutumin nan ya kwashe abin da ya faru duka tsakanin Abuƙir da marina, da yadda ya kai ƙarar su wurin Sarki duk ya gaya wa Abusir. Ya kuma ƙara da cewa, "da yake Sarki mutum ne mai son duk wani abu da zai kawo cigaba a garinsa, sai ya gina masa wannan marina da kake gani, ya saya masa komai na kayan aiki, babu dirhami ko ɗaya na marinin, ya kuma ba shi gida da bayi da dukiya mai yawa. Ka gani, da ma an ce idan an hana maraya rigar saƙi, sai Allah ya ba shi ta ƙarfe."


Yayin da Abusir ya ji wannan jawabi sai ya cika da farin ciki ya ce a cikin ransa, 'tsarki ya tabbata ga Allah da ya cika wa abokina burinsa na zama gwani ga sana'arsa. Da fari na zarge shi da mantawa da ni, ashe ba ya da laifi, ayyuka ne suka rufe shi har ya manta da ni, lallai yanzu na yi masa uzuri a kan haka. Bari in tafi gare shi, na tabbata zai yi farin ciki da sake gani na, zai tare ni da murna ya kyautata mini kamar yadda na kyautata masa lokacin da ba shi da aikin yi.' Sai ya kutsa cikin mutane, ya tasar wa ƙofar shagon. 


Tun daga nesa ya hangi Abuƙir cikin tufafi na alfarma, ya kame bisa kujera kamar wani Sarki. Ga bayi huɗu baƙaƙe da kuma wasu huɗu farare sun kewaye shi suna ta yi masa hidima. Ga kuma wasu bayi goma da ke ta aikin rini, wasu na tsoma tufafi, wasu na fitarwa, wasu na matsewa, wasu na shanyawa. Shi kuwa Abuƙir babu aikin da yake yi sai ba da umurni, a yi kaza, a yi kaza.


Wanzami ya matsa har ya zo kusa da ƙofar shagon, ya ja ya tsaya. Ya tabbata idan Marini ya gan shi, zai taso ya rungume shi cikin farin ciki, ya ja hannunsa ya zaunar da shi kusa gare shi, ya girmama shi, ya yi masa hidima. Sa'adda idanu biyu suka afku cikin idanu biyu, Abuƙir ya yi ido huɗu da Abusir


Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, insha Allah.


Me kuke tsammani zai faru tsakaninsu? Ko kuna ganin Abuƙir zai iya mai da buki?


Bukar Mada

15/10/2022

Comments