SHARRI KARE NE 2
HIKAYAR ABUƘIR MARINI DA ABUSIR WANZAMI
(Daga Littafin Dare Dubu Da Ɗaya)
Waziri Aku
Da Abuƙir ya ga ya shawo kan Abusir, har ya yarda za su shiga duniya neman arziki tare, sai ya yi farin ciki, gayar farin ciki. Ya ce wa Wanzami, "ya makwabcina, yanzu kam mun zama 'yan'uwa, babu wani bambanci a tsakaninmu. Sai mu yi wa juna alkawari cewa, idan muka bar garin nan, ran da duk ɗaya daga cikinmu bai samu aikin yi ba, to wanda ya samu aiki zai ciyar da shi. Sa'annan mu samu ƙaton asusu mu riƙa ɗan tsinkular abin da muka samu na kuɗi muna jefawa a ciki, ka san an ce ajiya maganin wata rana, ran da duk Allah ya maido mu gida lafiya, sai mu fashe shi, mu ga abin da Allah zai ba mu."
Abusir ya yi na'am da wannan shawara. Suka ɗauki alkawari. Suka kuma yi addu'a tare da fatar tsinuwar Allah ga duk wanda ya saɓa wannan alkawari, suka shafa Fatiha. Suka shirya barin garin washegari.
Da gari ya waye suka ƙulle 'yan kayansu, Abusir ya rufe shago ya danƙa wa masu shagon mabuɗinsu, shi kuwa Abuƙir bai ko kula da nasa shagon ba, ya bar mabuɗi ga Alƙali. Suka samu wani jirgin 'yan kasuwa da za su fatauci suka shiga, babu ɗayansu da yake da wani guzurin kirki. Jirgi ya miƙa cikin teku, suka ba Iskandariya baya, tun suna hangen gine-ginen birni har suka daina ganin ko ɓirɓishinsu.
Daga nan sai Abusir ya ce wa Abuƙir, "abokina, ka ga akwai tafiya mai nisa a gabanmu, ba na tsammani ɗan guzurin nan namu zai ishe mu. Bari na zagaya cikin jirgin nan da kayan aikina ko Allah ya sa na samu wanda zan yi wa aski ko ƙaho ya ba mu abinci."
Abuƙir ya ce, "wannan daidai ne ɗan uwana." Ya gyara shimfiɗa ya mimmiƙe abinsa.
Wanzami ya ɗauki zabirarsa, ya saɓa wani tsumman mayafi a kafaɗa, wanda yake yi wa mutane aski da shi, ya shiga cikin jirgi yana zagayawa. Jirgin nan kuwa na ɗauke da 'yan kasuwa ɗari da ashirin, inda kuma Allah ya tarfa wa garinsa nono, sai ya kasance babu wani wanzami a cikin jirgin sai shi kaɗai. Yana cikin zagayawa sai wani mutum ya sa baki ya kira shi, "kai wanzami, zo ka yi mini aski."
Abusir ya tsaya ya yi masa aski. Mutumin ya kawo rabin dirhami ya ba shi, sai ya ƙi karɓa ya ce, "abokina, da dai za ka ba ni abinci da ɗan ruwa da na so. Wanna kuɗi ba shi da wani amfani gare ni yanzu. Tare nake da ɗan uwana, kuma ba mu da isasshen guzuri."
Mutumin ya kawo gurasa da yankan burodi ɗaya, ya kuma cika masa wani ɗan gora da ruwa ya ba shi. Wanzami ya ɗauki abinci ya kai wa Marini ya ce, "ci wannan, bari na koma in ga abin da zan kuma samowa." Marini ya karɓe abinci ya cinye, ya sha ruwa. Ya gyara shimfiɗa ya yi kwanciyarsa.
Wanzami ya sake kutsawa cikin jirgi. Duk inda ya jefa ƙafa sai a kira shi domin ya yi aski. Aka yi ta ba shi abinci iri-iri, kamar su gurasa, ƙosai, burodi, dabino, soyayyen nama, ƙyafaffen kifi, madara, cukwi da sauransu. Da aka ga dai ya iya aski, sai aka soma yi masa layi, ga shi kuma babu wani wanzami a jirgin.
Aka ce kowa ya samu rana to ya kamata ya shanya garinsa kafin ta gushe, don haka sai ya riƙa yanka ladar abin da za a biya shi, maimakon a ba shi abinci kurum, sai ya riƙa haɗawa da kuɗi. Idan aka ba shi abinci, sai kuma a haɗa masa da rabin dirhami ko dirhami ɗaya. Don haka ko kafin rana ta faɗi, ya tara kaɓukkan abinci, ya kuma samu dirhami talatin ya ƙulle a mayani.
A cikin waɗanda ya yi wa askin nan har da madugun jirgin, watau shugaban matuƙa jirgi. Yayin da yake yi masa aski ne madugun ya tambaye shi, me ya sa ake biyansa da abinci?
Wanzami ya kwashe labarinsa da na abokin tafiyarsa ya faɗa masa. Da Madugu ya ji haka sai ya ce, "af, don wannan kada ku tayar da hankalinku. In don abinci ne, to kullum da yamma ku zo tantina mu ci tare har Allah ya sauke mu lafiya. Muna da isasshen abinci ni da ma'aikatana."
Yayin da ya dawo inda Marini, sai ya tarar da shi yana ta sharɓar barci. Ya tashe shi. Da Abuƙir ya buɗe ido ya ga garar da Wanzami ya kinkimo a cikin kwando, sai ya wangame baki cikin mamaki, ya tambaye shi, "ina ka samo wannan abinci haka?"
Abusir ya amsa masa, "wannan yana daga falalar Ubangiji mai girma."
Abuƙir ya jajjanye hannuwan riga zai far ma abinci da ci, Abusir ya ce masa, "ya ɗan uwana, mu adana wannan saboda amfanin gaba. Ka tashi yanzu maza mu tafi tantin Madugu mu ci abinci, domin na faɗa masa matsalarmu, ya kuma yi alkawarin ciyar da mu har ranar da muka sauka."
Abuƙir ya ce, "wallahi ɗan uwana ba ni da lafiya, masassarar teku ta kama ni, da zarar na miƙe tsaye sai jiri ya ɗebe ni, in ji kamar zan yi amai. Bar mani wannan abincin na ɗan taɓa kaɗan na adana mana saura, kai kuwa ka tafi wurin Madugu ku ci tare."
Abusir ya ce, "babu laifi ga haka." Ya miƙa masa abinci.
Marini ya sassauta ɗaurin ɗamarar da ta tanke cikinsa, ya gyara zama. Ya jawo kwandon abinci gabansa ya fara wurga loma, kamar ana wurga dutse a cikin rami, yana haɗiyewa kamar giwar da ta yi kwana da kwanaki ba ta haɗiyi komai ba. Kafin lomar ta faɗa har ya yanko wata yana shirin jefawa baka, yana kallon abincin sai ka ce maye na kallon mara lafiya. Wazami dai ya ƙura wa ikon Allah ido.
Za mu ci gaba.
Bukar Mada
05/10/2022